Harajin 0.5%: SERAP Na Shirin Maka Gwamnatin Tinubu Kotu Nan da Kwana 2

Harajin 0.5%: SERAP Na Shirin Maka Gwamnatin Tinubu Kotu Nan da Kwana 2

  • Kungiyar kare hakkin tattalin arziki (SERAP) ta baiwa gwamantin tarayya wa'adin sa'o'i 48 kan janye dokar harajin kudin tsaron yanar gizo
  • Kungiyar ta ce tabbas harajin zai kara jefa 'yan Najeriya cikin wahala da kuncin rayuwa kuma ya sabawa dokar kasa da hakkin dan Adam
  • Ta kuma tabbatar da cewa lauyoyin ta sun shirya tsaf domin daukan mataki na gaba idan gwamantin ta ki janye dokar cikin lokacin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kungiya mai kare hakkin tattalin arziki (SERAP) ta bukaci shugaba Bola Tinubu ya janye maganar saka harajin 0.5% ga abokan hulɗar bankuna.

Shugaba Bola Tinubu
SERAP ta ce harajin 0.5% na tsaron yanar gizo ya sabawa doka. Hoto: Aiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Kungiyar SERAP za ta yaki Tinubu

Kara karanta wannan

"Za mu dauki kwararan matakai kan barayin gwamnati", EFCC

SERAP ta ce kudirin ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa na 1999 kuma ya sabawa hakkin dan Adam da na zaman kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton gidan talabijin din Channels ya nuna cewa kungiyar ta ce dole ne shugaba Tinubu ya janye maganar harajin cikin sa'o'i 48.

Kungiyar ta kara da bukatar shugaban da ya gaggauta jan kunnen Nuhu Ribadu, mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, wurin zartar da dokar yaki da ta'addancin yanar gizo.

SERAP ta yi kira ga ministan shari'a

Har ila yau kungiyar ta yi kira ga ministan shari'a, Lateef Fagbemi, da ya gabatar da kudurin gyara sashe na 44 na dokar ta'addancin yanar gizo ta 2024.

Dokar ita ce ta ba hukumar damar karbar haraji a hannun kowane 'dan Najeriya wanda kungiyar ta ce hakan ya sabawa dokar kasa.

Kara karanta wannan

Kungiyar NECA ta yi kira ga gwamnatin tarayya kan karin albashin ma'aikata

Idan Tinubu bai janye dokar ba fa?

Kungiyar SERAP ta ce lauyanta, Ebun-Olu Adegboruwa ya shirya tsaf domin shigar da karar gwamnatin idan ta ki janye dokar, cewar jaridar Daily Post.

Ta kuma kara da cewa bai kamata ma shugaba Bola Tinubu ya yi gardama wurin janye dokar ba saboda ta saɓa da kundin da ya rantse da shi wurin kama aiki.

Gwamnatin tarayya ta kirkiro sabon haraji

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta umurci bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi a Najeriya da su fara karbar harajin kaso 0.5% daga kudaden da abokan hulda ke turawa.

Babban bankin Najeriya (CBN) ne ya bayar da wannan umarnin a jihar Litinin, 6 ga watan Mayu, tare da kakaba tarar kaso 2% idan ba a biya harajin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel