An Yi Kwamacala Yayin da Aka Rantsar da 'Yan Siyasa da Alkur'ani da Kuma Gunki

An Yi Kwamacala Yayin da Aka Rantsar da 'Yan Siyasa da Alkur'ani da Kuma Gunki

  • Mutane sun shiga mamaki bayan ganin rantsar da masu mukaman siyasa a jihar Ekiti da Alkur'ani hade da gunki
  • Lamarin ya faru ne a jihar Ekiti yayin da shugaban karamar Ikere-Ekiti, Olu Adamolekun ke rantsar da masu ba shi shawara
  • Adamolekun ya bukace su da su rike Alkur'ani da gunki da ake kira Ógún tare da yin biyayya ga gwamna da kuma jam'iyyar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ekiti - Shugaban karamar hukuma a jihar Ekiti ya rantsar da masu ba shi shawara na musamman kan harkokin gwamnati.

Sai dai rantsarwar ta zo da wani irin yanayi yayin da ya rantsar dasu da Alkur'ani da kuma ɗan karamin gunki.

Kara karanta wannan

An gurfanar da mutumin da ake zargi da safarar makamai ga 'yan bindiga a Kano

An rantsar da 'yan siyasa da gunki da kuma Alkur'ani
Shugaban karamar hukuma a Ekiti ya rantsar da hadimansa da Alkur'ani da kuma gunki. Hoto: Ajayi Rotimi Otunba.
Asali: Twitter

Yaushe aka yi rantsuwa da Alkur'ani, gunki?

Shugaban karamar hukumar Ikere-Ekiti, Olu Adamolekun shi ne ya rantsar da masu mukaman a ranar 2 ga watan Mayu, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wani faifan bidiyo da ke yawo, an gano wadanda ke karbar rantsuwar rike da Alkur'ani da kuma gunki da ake cewa Ógún.

Ógún na daga cikin ababan bauta na addinin gargajiya a Nahiyar Afirka da ke kira 'God of Iron'.

Yayin kama rantsuwar, Adamolekun ya bukace su da su rika maimaita bin da zai fada a taron kamar haka:

"Daga yau zan kasance mai biyayya kuma da gaskiya ga BAO (gwamnan jihar Ekiti) da Monisade (mataimakin gwamna) da APC da kuma shugabanninta."
"Zan rika daukar umarni daga gare su, idan kuma naƙi, Ógún ko Alkur'ani ya kashe ni, saboda haka zan zama mai gaskiya."

Kara karanta wannan

"Zai yi wahala": Lauyan APC ya fadi hanya 1 da Ganduje zai rasa muƙaminsa a jam'iyya

- Olu Adamolekun

Ana rantsuwa da Alkur'ani, Injila a Najeriya

A Najeriya, mafi yawan 'yan siyasa na rantsuwa ne da Alkur'ani ko kuma Injila da kuma biyayya ga kundin tsarin mulki.

Amma a wannan bidiyon, an bukaci masu mukaman su yi biyayya ga jam'iyyar APC da shugabanninta a jihar Ekiti wurin amfani da gunki.

Tsofaffin masu neman takara sun yi murabus

A wani labarin, kun ji cewa tsofaffin masu neman takara a jihar Edo daga jam'iyyun APC da APC sun yi murabus.

Wanda ya nemi takarar gwamna a PDP, Felix Akhabue ya watsar da ita yayin da 'yar takarar APC, Dakta Victoria Amu ita ma ta yi murabus..

Asali: Legit.ng

Online view pixel