'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 8 Tare da Sace Manajan Banki a Jihar Zamfara

'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 8 Tare da Sace Manajan Banki a Jihar Zamfara

  • Ƴan bindiga sun kai wasu sababbin hare-haren ta'addanci guda biyu a jihar Zamfara wacce ta daɗe tana fama da matsalar rashin tsaro
  • Miyagun ƴan bindigan sun hallaka mutum takwas a wani sabon hari da suka kai a garin Faru da ke ƙaramar hukumar Maradun ta jihar
  • A wani harin kuma, ƴan bindiga fiye da mutum 15 sun je har gida tare da yin garkuwa da manajan bankin Taj, a unguwar Rijiyar Gabas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun hallaka mutum takwas tare da yin garkuwa da manajan bankin Taj, Mandir Laura a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan waɗanda adadinsu ya kai kusan mutum 15, sun farmaki gidan manajan bankin ne da ke unguwar Rijiyar Gabas.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun hallaka mutum 2 da sace wasu da dama a Kaduna

'Yan bindiga sun hallaka mutane a Zamfara
'Yan bindiga sun sace manajan banki a Zamfara Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Yadda ƴan bindiga suka kai hari

Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa lamarin ya auku a daren ranar Litinin, sannan suka tafi da shi inda ba a san ko ina ne ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika wasu ƴan bindiga sun kai hari garin Faru da ke ƙaramar hukumar Maradun a jihar inda suka kashe mutum takwas.

Wasu daga cikin mazauna garin sun ce ƴan bindigan sai da suka zagaye garin kafin su ƙaddamar da ta’addancinsu a kan mutane.

Majiyoyin sun kuma ƙara da cewa ƴan bindigan sun yi awon gaba da mutane da dama cikin dajin da ke kusa da garin.

Me ƴan sanda suka ce kan harin?

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, Yazid Abubakar, domin samun ƙarin bayani kan hare-haren guda biyu.

Kakakin ya tabbatar da sace manajan bankin na Taj inda ya ce jami'an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin ganin an ceto shi inda ya ce akwai alamun nasara.

Kara karanta wannan

Miyagu sun tafka ɓarna, sun yi garkuwa da fasinjojin jirgin ruwa a Najeriya

Dangane da harin Faru, jami'in ya bayyana cewa bai samu tabbatarwa ba saboda matsalar rashin sabis da ake fama da ita.

Ƴan bindiga sun hallaka jami'an tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun yi wa jami’an rundunar tsaron jihar Zamfara (CPG) waɗanda aka fi sani da Askarawan Zamfara kwanton ɓauna.

Ƴan bindigan sun hallaka jami'ai uku bayan sun yi musu kwanton ɓauna a unguwar Jambako da ke ƙaramar hukumar Maradun ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel