Majalisa Ta Gayyaci Kamfanonin Siminti Domin Amsa Tambayoyi Kan Tashin Farashi

Majalisa Ta Gayyaci Kamfanonin Siminti Domin Amsa Tambayoyi Kan Tashin Farashi

  • Majalisar wakilai ta umurci manyan kamfanonin simintin Najeriya da su gurfana a gabanta nan da makwanni biyu
  • Gayyatar ta biyo bayan yin biris da shugabannin kamfanonin suka yi ne ga kiran da majalisar ta musu a karon farko
  • Legit ta tattauna da wani dilan siminti, Muhammad Babari domin jin yadda masu sana'ar za su kalli yadda dambarwar ke gudana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Biyo bayan hauhawar farashin kayayyaki, majalisar wakilai ta gayyaci manyan 'yan kasuwa domin neman mafita.

Majalisa
Majalisar wakilai ta gayyaci kamfanoni saboda tsadar siminti. Hoto: Hollie Adams
Asali: Getty Images

Majalisa za ta ji dalilin tashin siminti

Majalisar ta ba su kwanaki 14 su gurfana a gabanta domin yin bayani a kan dalilin tsadar siminti a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Kudurin Majalisa: Za a rika yankewa masu safarar miyagun kwayoyi hukuncin kisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton da jaridar Daily Trust ta fitar ya nuna cewa kamfanonin siminti da aka gayyata sun hada da simintin Dangote, BUA da IBETO.

Sabuwar gayyatar ta zo ne saboda kin amsa gayyatar majalisar da kamfanonin suka yi a yau Talata, cewar jaridar the Nation.

Kwamitin da majalisar ta kafa

Majalisar ta kafa kwamitin ne na musamman domin bincike kan dalilin tashin farashin siminti a fadin Najeriya.

Mambobin kwamitin sun hada da 'yan majalisa masu kula da kwamitin ma'adanai, kasuwanci, masana'antu da ayyukan yau da kullum.

Majalisa ta gayyaci ministan makamashi

Har ila yau, majalisar ta bukaci ministan makamashi, Dele Alake, ya gurfana a gabanta biyo bayan bijire wa gayyatar ta da ya yi.

Majalisar ta ce ministan makamashin zai gurfana a gabanta ranar Talata, 21 ga watan Mayu, sauran kamfanonin kuma za su zo ranar 20 ga wata.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun amince da hukuncin kisa kan masu safarar kwayoyi, an samu hatsaniya

Jawabin shugaban kwamitin majalisar

Shugaban kwamitin, Jonathan Gaza Gefwi, ya ce kin amsa gayyatar da suka yi a karon farko ya nuna basu damu da wahalhalun da 'yan Najeriya ke ciki ba.

Ya kuma kara da cewa yadda aka samu sauƙin farashin siminti a kasashe irinsu Kenya, India da Zambiya a shekarar 2021 ya nuna siminti ya fi tsada a Najeriya sama da ko ina.

Saboda haka ne ya ce lalle ya zama wajibi abi dukkan matakai domin saukaka farashin siminti a Najeriya.

Jawabi daga dilan siminti

Wani dilan saiminti a jihar Gombe, Muhammad Babari ya ce lalle idan gwamnati za ta saka baki to za a iya samun saukin farashin.

Amma duk da haka ya kara da cewa ba a nan gizo ke sakar ba, a cewarsa babbar matsalar daga manyan diloli take.

Ya bayyanawa Legit cewa idan ana son samun saukin farashi to dole gwamnati ta nemi manyan diloli bayan tattaunawa da kamfanonin.

Kara karanta wannan

N15tr: "Za mu binciki yadda aka ba da kwangilar titin Lagos-Calabar", Majalisa

Za a dauki mataki kan tsadar siminti

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce tana duba yiwuwar bude iyakokin kasar don fara shigowa da siminti da nufin karya farashinsa a kasuwanni.

Wannan gargadi ne da ministan gidaje da raya karkara, Arc. Dangiwa ya yi wa dukkan kamfanonin da ke sarrafa siminiti a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel