Iran Ta Sabunta Makamai Yayin Tsagaita Wuta da Amurka, Tana Shirin Ko Ta Kwana

Iran Ta Sabunta Makamai Yayin Tsagaita Wuta da Amurka, Tana Shirin Ko Ta Kwana

  • Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fara gyara makamanta da sabunta su yayin tsagaita wuta da ake yi da Amurka
  • An gyara na’urorin harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da suka samu matsala a yayin yakin Amurka da Isra'ila ke yi
  • Rikici ya sake ɗaukar zafi bayan batun rufe mashigar Hormuz da barazanar Amurka yayin da ake hasashen zaman sulhu ko zai yiwu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Iran –Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fara sake gina tarin makamanta da harsasai a lokacin tsagaita wuta da aka cimma da Amurka da taimakon Pakistan.

Wani babban jami’in soji na kasar, Brigediya Janar Seyed Majid Mousavi, kwamandan rundunar sararin samaniya ta dakarun IRGC ne ya tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

Iran ta kafe kan sharadin sulhu da Amurka, ta yi fatali da tsagaita wuta na wucin gadi

Iran ta ci gaba da shirin yaƙi a Gabas ta Tsakiya
Wasu makamai masu linzami da Iran ta harba kan birnin Tel Aviv na Isra'ila. Hoto: Mostafa Alkharouf/Anadolu via Getty Image
Source: Getty Images

BBC Hausa ta wallafa cewa babban jami'in ya ce ce an gyara na’urorin harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa tun daga ranar 8 ga Afrilu, 2027 , lokacin da aka fara tsagaita wuta.

Iran ta gyara makamanta

International Business Times ta ruwaito Brigediya Janar Seyed Majid Mousavi, ya ce Iran na hanzarta sabunta kayan yaƙinta fiye da yadda take yi kafin rikicin ya barke.

Ya bayyana cewa ƙasar na ƙara ƙarfi cikin sauri domin kasancewa cikin shiri idan rikicin ya sake ɓarkewa a Gabas ta Tsakiya.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ke sake ƙamari, bayan Iran bayan Iran ta sanar da rufe mashigar ruwan Hormuz, duk da cewa a baya ta ce za ta bar ta a buɗe yayin tsagaita wuta.

Rahotanni sun ce dakarun Iran sun harba makamai kan wasu jiragen ruwa da suka yi ƙoƙarin wucewa ta wannan muhimmin mashiga, bayan Amurka ta yi babakere a iyakokin tekunta.

Kara karanta wannan

Italiya ta datse yarjejeniyar sayar wa Isra'ila makamai kan yakin Lebanon

Trump ya sake barazana ga Iran

Donald Trump ya ce an kai wasu daga cikin hare-haren kan jirgin Faransa da kuma wani jirgin kasuwanci daga Birtaniya.

Trump ya sabunta barazana ga Iran
Shugaban Amurka Donald J Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

Trump ya kuma jaddada cewa rufe mashigar ba zai shafi Amurka sosai ba, yana mai cewa jiragen ruwa da dama na kan hanyarsu zuwa jihohin Texas, Louisiana da Alaska domin ɗaukar kaya.

Ya yi gargadin cewa Amurka na ba Iran wata dama mai kyau ta cimma yarjejeniya. Amma idan ta ƙi, ya ce Amurka za ta lalata muhimman ababen more rayuwa kamar tashoshin wutar lantarki da gadaje.

Ya ƙara da cewa, idan Iran ba ta amince da yarjejeniya ba, zai ɗauki matakin da ya dace, yana mai cewa lokaci ya yi da za a ɗauki tsauraran matakai kan ƙasar.

Dalilin Trump na fara yaƙi da Iran

A baya, mun wallafa cewa tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris, ta taso Shugaba Donald Trump a gaba kan yakin da ya fara da Iran.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwan da suka faru bayan tsagaita wutar Iran, Amurka da Isra'ila

Kamala Harris ta bayyana cewa akwai abin da Donald Trump yake son karkatar da hankalin jama'a kansa, shiyasa ya fara yaki da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Tsohuwar 'yar takarar shugaban kasar ta bayyana cewa Firaministan Israila, Benjamin Netanyahu ne ya ja hankalin Trump kan yakin domin a haɗa kai a rufe batun Epstein.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng