An Yi Babban Rashi a Jihar Kano, Tsohon Shugaban NFF Ta Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Tsohon shugaban hukumar NFF, Alhaji Ibrahim Galadima ya riga mu gidan gaskiya yana da ahekaru 78 a duniya
- Marigayi Galadima, wanda ya kafa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ya rasu bayan fama da doguwar jinya a gida da asibiti
- Hukumar NFF ta yi alhinin wannan rashi, inda ta bayyana marigayin a matsayin uba, wanda ya ba da gudummuwa mai tarin yawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Tsohon shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFA), wadda yanzu ake kira NFF, kuma wanda ya kafa ƙungiyar Kano Pillars, Alhaji Ibrahim Galadima, ya rasu.
Galadima ya rasu ne a ranar Asabar, 18 ga watan Afrilu, 2026 yana da shekaru 78 da haihuwa, bayan shafe tsawon lokaci yana jinya.

Source: Facebook
Tsohon shugaban NFF, Galadima ya rasu
Tsohon babban sakataren NFF, Sani Toro, ne ya fara tabbatar da rasuwar, inda ya bayyana cewa marigayin ya rasu a Kano, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
“Ina bakin cikin sanar da rasuwar Alhaji Ibrahim Galadima, tsohon shugaban NFA, a yau a Kano. Allah ya jikansa da rahama, ya sa ahi a gidan Aljannatul Firdausi,” in ji Toro.
A cikin wata sanarwa, hukumar NFF ta bayyana Galadima a matsayin ɗaya daga cikin fitattun masu gudanar da harkokin wasanni a Najeriya, tare da yabawa igudunmawar da ya bayar tsawon shekaru.
Mukaman da Galadima ya rike
Marigayin ya riƙe muƙamin shugaban NFA daga shekarar 2002 zuwa 2006, lokacin da aka samu sauye-sauye a tsarin gudanarwa da kuma ci gaba da wakilcin Najeriya a matakan nahiyar Afirka da duniya.
Kafin ya zama shugaban NFA, ya rike mukamai daban-daban a harkar wasanni, ciki har da shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Jihar Kano da kuma shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano.
Haka kuma ya taɓa zama mataimakin shugaban farko na Kwamitin Olympics na Najeriya, tare da kasancewa cikin kwamitin da ya sa ido kan gina filayen wasa kafin gasar FIFA World Youth Championship ta 1999 da Najeriya ta karɓi bakunci.

Source: Getty Images
Shugaban NFF ya mika sakon ta'aziyya
Shugaban NFF, Ibrahim Gusau ya nuna alhini matuƙa, yana mai cewa Galadima ya kasance jagora kuma uba ga da dama daga cikin shugabannin wasanni na yanzu.
“Wannan babban rashi ne gare mu. Alhaji Ibrahim Galadima ya kasance malami ga da yawa daga cikinmu. Ya kasance mutum mai mutunci, ƙwazo da gaskiya."
“Za mu yi kewar shawarwarinsa da hikimarsa. Muna roƙon Allah Ya gafarta masa, Ya ba iyalansa da dukkan al’ummar ƙwallon ƙafa a Najeriya haƙurin jure wannan babban rashi,” in ji Gusau.
Daily Trust ta rahoto cewa za a yi sallar jana’izarsa a ranar Lahadi da ƙarfe 10:00 na safe a Masallacin Waje da ke ƙaramar hukumar Fagge a Jihar Kano.
Kanin Sarkin Kano ya kwanta dama
A wani labarin, kun ji cewa Salihi Aminu Sanusi, ƙanin Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya riga mu gidan gaskiya.
A sanarwar da ta fitar, masarautar Kano ta bayyana jimaminta bisa wannan rashi, kuma tuni aka yi masa sallar jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Mutane da dama sun nuna alhini tare da yin addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta masa kura-kuransa, ya jiƙansa da rahama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

