Gwaji Kafin Aure: Gwamna Abba ya Sanya Hannu kan Dokar Tilasta Gwajin Cututtuka

Gwaji Kafin Aure: Gwamna Abba ya Sanya Hannu kan Dokar Tilasta Gwajin Cututtuka

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan dokar tilasta gwajin wasu cututtuka kafin aure domin rage yaduwar cutuka
  • Daga gwaje-gwajen da za a yi akwai na cuta mai karya garkuwar jiki watau HIV/AIDS, da na ciwon hanta, da gwajin jini domin gano masu cutar sikila
  • Za a hukunta duk limamin da ya daura aure ba shaidar gwajin asibiti da tarar N500,000, ko daurin shekaru biyar, ko a hada masa duka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano-Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ta rattaba hannu kan dokar tilasta gwaji kafin aure domin tsaftace auren da kare ‘ya’yan da za a haifa daga cutukan da za a iya karewa.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida ya kaddamar da titi mai hawa 3 a kan kudi ₦15bn a Dan Agundi

Daga cikin gwaje-gwajen da za a yi kafin auren har da na cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDS, da na ciwon hanta, da gwajin jini domin tantance wadanda ke dauke da cutar sikila.

Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir ya sanya hannu kan dokar tilasta gwaji kafin aure a Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Gwajin aure ya zama dole a Kano

A sanarwar da Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya a shafinsa na facebook, ya ce an tilasta gwaje-gwajen ne domin rage haihuwar yara dauke da cutukan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce za a ci tarar duk wanda aka kama da saba dokar N500, 000 ko daurin shekara biyar. Haka kuma gwamnatin ta haramta kyamar masu dauke da wadannan cutar.

Gwamnan ya sanya hannu kan dokar ne a jiya Litinin, kuma za ta fara aiki ne a ranar 13 ga watan Mayu 2024.

Yanzu a jihar Kano, an haramta daura aure ba tare da shaidar lafiya daga asibitin da ake amince da shi ba.

Kara karanta wannan

'Akwai manyan da ke yi wa gwamnatina makarkashiya', Gwamnan APC ya koka

Menene hukuncin karya dokar gwajin aure?

A cewar sanarwar da Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu a yau Talata, duk limamin da aka samu ya daura aure ba tare da takardar shaidar lafiya ba ka iya fuskantar tarar N500, 000.

Za kuma a iya yiwa limamin daurin shekaru biyar, ko a hada masa tarar N500, 000 da daurin shekarun, kamar yadda Kanofocus ta wallafa.

Gwamnatin na ganin daukar matakin zai rage yiwuwar haihuwar yara dauke da cutukan sikila da HIV/AIDS, da ciwon hanta.

Daliba ta aure mijin tsohuwar malamarta

Mun ruwaito muku a baya cewa wata uwargida ta jinjinawa mai gidanta bayan ya auri tsohuwar dalibarta, tare da yaba masa saboda bai boye mata ba.

Fatima Yusuf Nuhu, wacce ita ce uwargidan ta gayyaci jama’a su zo daurin auren domin ta bayyana cewa tana cikin jin dadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel