Aikin Hajji: Abba Ya Cika Alkawari, NAHCON ba ta bin Maniyyatan Kano Sisin Kobo

Aikin Hajji: Abba Ya Cika Alkawari, NAHCON ba ta bin Maniyyatan Kano Sisin Kobo

  • Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta bayyana kammala biyan kudin dukkanin maniyyatanta ga hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON.
  • Darakta Janar a hukumar, Alhaji Lamin Rabi'u Danbappa ne ya bayyana hakan, inda ya ce maniyyata 3,110 suka kammala biyan kudin aikin hajjin bana
  • Daraktan ya kara da cewa gwamnatin Kano ta koka kan yadda har yanzu hukumar NAHCON ta gaza baya maniyyata kimanin 1300 takardar izinin shiga kasar Saudiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano- Darakta Janar na hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya ce sun biya Naira biliyan 18 ga hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON.

Kara karanta wannan

JAMB 2024: Lauya ya ja hankalin gwamnati kan hana dalibai masu hijabi rubuta UTME

Alhaji Lamin Rabi’u ya bayyana cewa maniyyata 3110 ne suka nemi kujerar aikin hajjin, amma da yawa daga cikinsu na jiran takardar izinin shiga Saudiyya daga NAHCON.

Aikin hajjin bana
Hukumar jin dadin alhazai ta ce ta kammala biyan kudin alhazai ga hukumar ta kasa Hoto: Kano State Pilgrims Welfare Board
Asali: Facebook

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman A. Dederi ya tabbatarwa Legit Hausa cewa yanzu NAHCON ba ta bin jihar Kano ko sisi na aikin hajjin bana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Duk abun da ake so mu biya, mun biya hukumar alhazai ta kasa. Ba ta binmu ko kwabo,” a cewar shugaban.

Maniyyata 1300 ke jiran takardar biza a Kano

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta bayyana cewa har yanzu maniyyatan aikin hajjin bana kimanin 1300 ne ke jiran takardar izinin shiga Saudiyya.

Darakta Janar na hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan a Kano, inda ya roki hukumar NAHCON ta gaggauta mika takardun ga maniyyatan kafin a rufe.

Kara karanta wannan

Badakalar N80bn: Abin da wasu tsofaffin gwamnoni ke cewa game da Yahaya Bello

Shugaban ya kara da rokon hukumar NAHCON da ta bawa maniyyatan kudin guzurinsu a hannu, domin da yawa daga cikin maniyyatan za su sha wahala wajen zarar kudin ta katin ATM a Saudiyya.

Ya yi alkawarin gwamnatin Kano, karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf zai kammala gyara masaukin maniyyatan kafin fara jigilar alhazai.

Matashi ya samu kujerar aikin hajji

A baya kun ji cewa wani mahaddacin al'qur'ani a jihar Kano, Jafar Yusuf mai shekaru sha shida ya samu kyuatar kujerar aikin hajjin bana.

Gwamnatin jihar Kano ce ta karramar yaron ta hannun hukumar jin dadin alhazai saboda kwazo da ya nuna wajen gwanancewa da haddar al'qur'ani mai tsarki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel