An Shiga Jimami Bayan Nuhu Ribadu Ya Yi Babban Rashi a Rayuwarsa

An Shiga Jimami Bayan Nuhu Ribadu Ya Yi Babban Rashi a Rayuwarsa

  • Ɗan uwan mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya koma ga mahaliccinsa bayan ya yi rashin lafiya
  • Salihu Ahmadu Ribadu ya yi bankwana da duniya ne a ranar Lahadi, 5 ga watan Mayun 2024 a birnin Yola, babban birnin jihar Adamawa
  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da tawaga ta musamman domin yi wa Nuhu Ribadu ta'aziyyar wannan babban rashin da ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Adamawa - Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu, ya yi rashin ɗan uwansa, Salihu Ahmadu Ribadu.

Salihu Ahmadu Ribadu wanda ba shi da lafiya, ya rasu ne a Yola, babban birnin jihar Adamawa a ranar Lahadi, 5 ga watan Mayun 2024.

Kara karanta wannan

Tinubu yana kasar waje saboda rashin lafiya? Minista ya fadi gaskiya

Nuhu Ribadu ya rasa dan'uwansa
Bola Tinubu ya aika da tawagar yi wa Nuhu Ribadu ta'aziyya Hoto: Nuhu Ribabu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu ya yi wa Ribadu ta'aziyya

Bayo Onanuga mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru a wata sanarwa a shafinsa na X ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika da tawaga ta musamman domin yi wa Nuhu Ribadu ta'aziyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tawagar ta kasance a ƙarƙashin jagorancin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila.

Da yake magana a gidan Ribadu da ke Yola, shugaban ma'aikatar fadar shugaban ƙasan ya ce Shugaba Tinubu ya yi jimamin rasuwar wacce ya bayyana a matsayin abin baƙin ciki.

"Shugaban ƙasa ya yi umurnin mu zo Yola domin yi wa ɗaya daga cikin na kusa da shi ta'aziyya, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro da sauran iyalansa kan babban rashin da suka yi."
"Rashin ɗan uwa na kusa irin wannan abin baƙin ciki ne sannan yana da kyau abokai da ƴan uwa su zo su yi ta'aziyya ga iyalan da suka yi rashin."

Kara karanta wannan

Daga karshe an bayyana lokacin dawowar Tinubu gida Najeriya

- Femi Gbajabiamila

Tawagar ta'aziyyar Ribadu a Yola

Femi Gbajabiamila ya samu rakiyar mataimakin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hadejia, ministan yaɗa labarai, Alhaji Mohammed Idirs da ministan ilmi, Farfesa Tahir Mamman.

Sauran su ne ministar fasaha da tattalin arziƙin fikira, Hannatu Musa Musawa, ƙaramin ministan lafiya, Dr. Tunji Alausa da mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan ayyuka (ofishin mataimakin shugaban ƙasa), Dr. Aliyu Modibbo Umar.

Tsohon shugaban NLC ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Ali Chiroma, ya riga mu gidan gaskiya.

Ali Chiroma ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri (UNIMAID) da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno ranar 2 ga watan Afrilun 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel