"Laifinku Ne": Shehu Sani Ya Fadi Dalilin Ƙaƙaba Harajin 0.5% da CBN Ya Yi

"Laifinku Ne": Shehu Sani Ya Fadi Dalilin Ƙaƙaba Harajin 0.5% da CBN Ya Yi

  • Sanata Shehu Sani ya yi shaguɓe ga 'yan Najeriya kan jawowa kansu haraji na musamman daga babban bankin CBN
  • 'Dan siyasar ya ce laifin 'yan Najeriya ne inda suka yi ta korafe-korafe kan inda Bola Tinubu ya ke bayan kammala taro a Saudiyya
  • Sanatan ya na magana ne kan ƙaƙaba harajin 0.5% da Babban Bankin Najeriya, CBN ya yi kan masu tura kudi bankuna

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Yayin da ake ta cece-kuce kan sabon haraji da bankin CBN ya saka, Sanata Shehu Sani ya yi martani.

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya ya zargi 'yan Najeriya da jawo matsalar karin harajin da babban bankin CBN ya yi.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban kasa ya bukaci shugabanni su yi koyi da marigayi Yar'adua

Shehu Sani ya magantu kan haraji da CBN ya saka
Shehu Sani ya yi shaguɓe ga 'yan Najeriya kan harajin da bankin CBN ya saka. Hoto: Shehu Sani, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Shehu Sani ya magantu kan harajin CBN

Shehu Sani ya byyana haka a shafinsa na X a yau Talata 7 ga watan Mayu bayan karin haraji da bankin ya sanar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce 'yan Najeriya sun yi ta korafi kan inda Shugaba Bola Tinubu ya ke yayin da ya ziyarci wani taro a kasar Saudiyya.

Har ila yau, Kwamred Shehu Sani ya ce korafe-korafen da suke ta yi ne ya jawo aka kawo musu sabon haraji a kasar.

"Shugaban kasa ya yi tafiya, kun zo kuna ta damunsa ina ya shiga."
"Ga shi yanzu kun jawowa kanku haraji, sai ku sake tambayarsa yaushe zai dawo."

- Shehu Sani

An yi ta korafin inda Tinubu yake

Martanin na Shehu Sani na zuwa ne kwanaki kadan bayan 'yan Najeriya sun fara binciken Tinubu bayan kammala taron Saudiyya amma bai dawo ba.

Kara karanta wannan

CBN ya lissafo jerin hada hadar kudi 16 da harajin 0.5% ba zai shafa ba

A yau Talata 7 ga watan Mayu bankin CBN ya saka dokar biyan harajin har 0.5% domin tsaron yanar gizo a kasar.

Sai dai CBN ya ware wasu hada-hadar kudi 16 da wannan doka ba za ta shafa ba da suka haɗa da biyan albashi da karba ko biyan bashi.

CBN ya kakaba dokar biyan harajin 0.5%

Kun ji cewa Babban Bankin Najeriya, CBN ya kakabawa 'yan Najeriya sabon haraji kan hada-hadar kudi da za su yi.

Bankin ya kara akalla 0.5% kan kowane tura kudi da 'yan kasar zasu yi tsakaninsu domin tsaron yanar gizo.

Wannan na zuwa ne yayin da 'yan kasar ke kokawa kan tsare-tsaren Shugaba Bola Tinubu da ke jefa su cikin mawuyacin hali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel