An Budewa Jirgin Faransa Wuta da zai Wuce Ta Hormuz da Iran Ta Toshe

An Budewa Jirgin Faransa Wuta da zai Wuce Ta Hormuz da Iran Ta Toshe

  • An budewa wani jirgin ruwan Faransa wuta yayin da ya nufi wucewa ta mashigar Hormuz da dakarun Iran suka sanar da rufe shi ranar Asabar
  • Rundunar sojin Iran ta bayyana cewa ta rufe mashigar ne bayan ajiye sojoji da Amurka ta yi a kusa da Oman domin hana jiragenta wucewa
  • Yayin da ake kokarin kawo karshen yakin ta tattaunawa a Pakistan, Iran ta ce ba za ta koma teburin sulhu ba sai a cika sharudan da aka kafa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Wani jirgin ɗaukar kaya da kamfanin jigilar kaya na Faransa, CMA CGM, ke sarrafawa ya fuskanci abin da aka bayyana a matsayin harbe-harben gargadi.

Ya fuskanci harbe-harben ne yayin da yake wucewa ta mashigar Hormuz kamar yadda kamfanin ya sanar a ranar Lahadi, 19 ga Afrilun 2026.

Kara karanta wannan

Iran ta sake rufe mashigar Hormuz bayan ta zargi Trump da karya sharadi

Jirgin ruwa dauke da tutar kasar Faransa
Wani jirgin ruwa da aka tsare a kasar Faransa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Halin da matukan jirgin ke ciki

Rahoton Anadolu Agency ya tabbatar da cewa kamfanin ya ce dukkan ma’aikatan jirgin suna cikin ƙoshin lafiya kuma babu wanda ya ji rauni.

Kamfanin ya bayyana sunan jirgin a matsayin CMA CGM Everglade, kuma yana dauke da tutar Faransa a lokacin da aka kai masa harin.

Ƙungiyar Kula da Harkokin Jiragen Ruwa ta Duniya (IMO) ta ce jirgin ya samu matsala a Arewacin Kumzar, ƙasar Oman, sai dai ba a bayyana girman illar ba.

Jirgin Faransa na aiki bayan harbin

A cewar bayanin da kamfanin ya fitar daga baya, ya ce jirgin har yanzu yana aiki, inda lalacewar ta takaita ne ga wasu kwantena kawai.

Jirage da dama, ciki har da Everglade, sun ba da rahoton cewa sojojin Iran sun bude musu wuta bayan Tehran ta janye matsayarta kan sake bude mashigara Hormuz.

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron
Emmanuel Macron na amsa wayar tarho. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cewar jami’an Iran, an sake rufe hanyar ruwan ne a matsayin martani ga ci gaba da takunkumin da Amurka ke kakaba wa tashoshin jiragen ruwan kasar.

Kara karanta wannan

A karon farko bayan bude Hormuz, an hango jirgin mai na wuce wa ta Iran

Sai dai an bayyana cewa babba abin da ya fi tayar da hankali shi ne rashin tabbas kan halin da jirage za su shiga yayin da ake cigaba da samun rashin jituwa tsakain Iran da Amurka.

Tattaunawar Iran da Amurka a Pakistan

Da yake amsa tambaya kan yiwuwar sabon zagayen tattaunawa da Amurka, Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Saeed Khatibzadeh, ya ce ba za a iya gudanar da su ba har sai bangarorin biyu sun amince da wani tsari na bai daya.

“Har sai mun amince da tsarin, ba za mu iya sanya rana ba,”

In ji Khatibzadeh a hira da Al-Jazeera

Saeed Khatibzadeh ya jaddada cewa duk abin da Iran za ta amince da shi a tattaunawa dole ne ya kare hakkokinta karkashin dokar kasa da kasa.

Iran ta tarwatsa 'yan leken asiri

A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar sojin Iran ta sanar da cewa ta tarwatsa wani gungun masu leken asiri ga kasashen waje.

Bayanan da aka fitar sun nuna cewa ana zargin mutanen da aka tarwatsa na yi wa Isra'ila, Amurka da Birtaniya leken asiri ne a Tehran.

Hakan na zuwa ne yayin da wa'adin tsagaita wuta da kasashen suka yi na mako biyu ke shirin karewa, inda ba a san matakin da za a dauka ba bayan shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng