Abia: Tsohon Shugaban Majalisa, Tsofaffim Ciyamomi da Ƙusoshi Sun Fice Daga PDP

Abia: Tsohon Shugaban Majalisa, Tsofaffim Ciyamomi da Ƙusoshi Sun Fice Daga PDP

  • Wasu manyan ƙusoshin PDP sama da 20 sun fice daga jam'iyyar a cikin kwanaki uku da suka gabata a jihar Abia da ke Kudu maso Gabas
  • Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar da tsofaffin ciyamomi na cikin waɗanɗa suka sauya sheka daga PDP, suna shirin komawa APC
  • Sai dai jam'iyyar PDP ta bayyana lamarin da wata babbar alama da ke nuna za a haifi sabuwar jam'iyyar da za ta ba mara ɗa kunya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Abia - Manyan jiga-jigan Peoples Democratic Party (PDP) aƙalla 20 ne suka sanar da ficewarsu daga jam'iyyar cikin kwanaki uku a jihar Abiya.

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, ana kyautata zaton cewa manyan ƴan siyasan na shirin shiga wasu jam'iyyun siyasa nan ba da jimawa ba bayan sun baro PDP.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta fusata, ta umurci majalisar dokoki ta tsige gwamna nan take

Jam'iyyar PDP.
PDP ta rasa manyan kusoshi akalla 20 a jihar Abia Hoto: OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Idan ba ku manta a mako biyu da suka wuce, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma tsohon mataimakin shugaban majalisar dokokin Abia, Cosmas Ndukwe, ya bar PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban ɗan siyasar ya fice daga PDP ne tare da dukkan shugabannin jam'iyyar na gundumarsa da ke yankin ƙaramar hukumar Bande a jihar Abiya.

Jiga-jigan da suka bar PDP a Abia

A kwana biyu zuwa uku da suka wuce, tsohon shugaban majalisar dokokin Abia, Cif Chinedum Orji da tsohon mai tsawatarwa a majalisar, Ikechukwu Nwabeke, sun raba gari da PDP.

Sauran waɗanda suka fice daga PDP tare da su sun haɗa da tsofaffim ciyamomin kananan hukumomin Isuikwuato, Isiala Ngwa ta kudu da tsofaffin ƴan majalisar jiha.

Wace jam'iyya za su koma daga PDP?

Duk da waɗannan jiga-jigai ba su bayyana jam'iyyar siyasar da za su koma ba, amma wata majiya ta shaida wa jaridar Vanguard cewa sun gama shirin shiga APC.

Kara karanta wannan

Miyagu sun tafka ɓarna, sun yi garkuwa da fasinjojin jirgin ruwa a Najeriya

Yawancin wadanda suka sauya sheka suna ci gaba da kauracewa jam'iyyar Labour Party mai mulki a jihar Abia.

Da yake martani kan ficewar ƴaƴan jam'iyyar, kakakin PDP na jihar Abia, Elder Amah Abraham ya ce abin da ke faruwa wata alama ce da ke za a haifi sabuwar PDP.

APC ta nemi a tsige Gwamna Fubara

Rahoto ya zo cewa Jam'iyyar APC ta buƙaci majalisar dokokin jihar Ribas ta fara shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara daga kan mulki nan take.

Jam'iyyar APC ta ɗauki wannan matakin ne biyo bayan kalaman da Fubara ya yi kan sulhun da Tinubu ya masu a rikicin siyasar Ribas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262