Rikicin Siyasa Ya Ɓarke a Oyo, 'an Biya N1bn a Tsige Gwamna'
- Rikicin siyasa ya girgiza jihar Oyo inda aka zargi shirin tsige gwamna Seyi Makinde tare da biyan makudan kudi
- Majalisar dokokin Oyo ta rikice yayin zaman PDP, inda ‘yan majalisa suka kasu gida biyu kan zargin tsige shugaban majalisa Adebo Ogundoyin
- Makinde ya shiga tsakani ya daidaita rikicin, yayin da ake ta rade-radin rikici da fada tsakanin gwamnati da sarauta, ciki har da zargin sauke Olubadan
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Ibadan, Oyo - Rikicin siyasa ya dabaibaye Oyo a makon da ya gabata, yayin da ake zargin ana kulla makircin tsige gwamna.
Wasu majiyoyi sun ce an ware Naira biliyan daya a matsayin cin hanci domin raba gwamnan da kujerarsa.

Source: Facebook
Rigimar siyasa ta kunno kai a Oyo
Ana cikin rikicin akwai gwamna Seyi Makinde, shugaban majalisa Adebo Ogundoyin, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan
Atiku ya kare kansa kan zargin cin hanci, ya tuna baya kan abin da Obasanjo ya yi maaa
Har ila yau, rigimar ta shafi Olubadan, Oba Rashidi Ladoja, tare da manyan ‘yan siyasa da suka kara rikita al’amura.
Rikicin ya fara ne daga rade-radin sabani a majalisar dokokin Oyo, amma cikin sauri ya rikide zuwa babbar matsala mai shafar majalisa, bangaren zartarwa da kuma sarauta.
A zaman jam’iyyar PDP da aka shirya gudanarwa, majalisar ta rikice inda aka samu zazzafar muhawara tsakanin ‘yan majalisa kan zargin shirin tsige shugaban majalisa.
Majiyoyi sun ce yanayin ya kasance mai cike da tashin hankali, inda ‘yan majalisa suka kasu gida biyu kan batun tsige shugaban majalisa da tasirinsa.
Wasu ‘yan majalisa sun nuna adawa da kokarin tsige Ogundoyin, yayin da wasu ke goyon bayan sauya shugabanci a majalisar bisa wasu dalilai na siyasa.
An kuma zargi wasu masu karfi a bangaren gwamna da goyon bayan kokarin cire shugaban majalisa, duk da cewa ba a tabbatar da wannan zargi ba.
Haka kuma an yi zargin cewa akwai wani shiri na tsige gwamna Makinde da kudin cin hanci har N1bn, wanda ya tayar da hankali a siyasar jihar.

Source: Facebook
Majalisa ta magantu kan shirin tsige Makinde
Shugaban majalisar ya jaddada biyayyarsa ga Seyi Makinde da jam’iyyar PDP, yana cewa ba zai shiga wani shiri da zai tayar da rikici ba.
Wasu majiyoyi sun ce ainihin manufar rikicin ita ce rage tasirin Ogundoyin, musamman ganin ana danganta shi da burin zama gwamna nan gaba.
An ce ziyararsa ga Olubadan domin neman shawara kan burin gwamna ta tada hankalin wasu ‘yan majalisa da ke ganin yana kara karfi, cewar The Guardian.
Sai dai majiyoyi sun ce Ogundoyin ya yi taka-tsantsan kuma bai fada cikin tarkon da zai iya kawo sabani tsakaninsa da gwamna ba.
A gefe guda kuma, tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose ya zargi Makinde da kokarin sauke Olubadan, lamarin da ya kara tayar da kura.
Sai dai Olubadan ya musanta wannan zargi, yana cewa yawancin abubuwan da ake ji jita-jita ne kawai kuma babu wata barazana ga sarautar.

Kara karanta wannan
An zo wajen: Akpabio ya fasa kwai, ya fallasa masu daukar nauyin matsalar rashin tsaro
Gwamna Makinde zai tallafa wa ma'aikatan Oyo
A baya, mun rahoto cewa gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde ya amince da wasu kudi domin tallafa wa ma'aikatan jihar saboda tsadar man fetur.
Gwamnati ta bayyana cewa wannan matakin zai fara aiki na tsawon watanni uku domin rage wahalar rayuwa da jama'a suka shiga.
An dauki wannan mataki ne bayan tashin farashin man fetur a Najeriya wanda ya samo asali daga tsadar da mai ta yi a duniya.
Asali: Legit.ng
