Latest
Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ayyana kujerar marigayi Hon. Isa Dogonyaro babu kowa bayan ya rasu a ranar Juma'a da ta gabata a birnin Abuja.
Sojojin Najeriya sun kama barayin danyen mai da rijiyoyin bogi sama da biyar da kuma danyen mai lita 45,000 a Ribas. Laftanal Kanal Ishaya Manga ne ya bayyana hakan.
Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya ziyarci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin yi masa bayani kan halin tsaro a jihar Kogi da kuma wasu abubuwa.
Rundunar ƴan sandan Kano ta bayyana cewa a yanzun mutum takwas ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon harin da aka kai masallaci a ƙaramar hukumar Gezawa.
Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya sanar da mutuwar mataimakin shugaban ma'aikatansa, Gboyega Soyannwo bayan ya sha fama da jinya a yau Laraba.
Rikici ya kaure tsakanin wasu masu baban bola da mutanen unguwar Byazhin da ke kauyen Kubwa a karamar hukumar Bwari da ke babban birnin tarayya Abuja.
Babbar kotun tarayya mai zama a Maitama a Abuja ta amince da ba da belin tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele bayan ya musanta laifukan da ake tuhumarsa.
Bayanai sun nuna ‘Yan majalisar Najeriya za su tashi da kusan Naira biliyan 50 daga cikin baitul-mali a shekarar 2024 a matsayin albashi da alawus.
Limaman Musulunci sun sha alwashin ci gaba da shirinsu kan aurar da mata marayu guda 100 da suka yi niyya a karamar hukumar Mariga a jihar Niger.
Masu zafi
Samu kari