"Ba Ka da Lissafi Ko Kadan": Kungiyar TUC Ta Ɗaga Yatsa Ga Tinubu Kan Karin Albashi

"Ba Ka da Lissafi Ko Kadan": Kungiyar TUC Ta Ɗaga Yatsa Ga Tinubu Kan Karin Albashi

  • Kungiyar kwadago ta TUC ta caccaki Gwamnatin Tarayya kan gabatar da N48,000 a matsayin mafi karancin albashi a Najeriya
  • TUC ta ce gabatar da wannan a matsayin mafi karancin albashi rashin hankali ne da rashin lissafi a halin da ake ciki
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wasu ma'aikata kan gabatar da mafi karancin albashin N48,000 da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar kwadago ta TUC ta yi fatali da tayin Gwamnatin Tarayya kan mafi karancin albashi.

TUC ta ce kwata-kwata babu hankali kan gabatar da N48,000 da gwamnatin ta yi a matsayin mafi karancin albashi.

Kara karanta wannan

"N48,000 Tayin almajirai ne": Shehu Sani ya caccaki gwamnati kan mafi karancin albashi

Kungiyar TUC ta caccaki Tinubu kan mafi karancin albashi
Kungiyar TUC ta yi fatali da gabatar da mafi karancin albashin N48,000 da Bola Tinubu ya yi. Hoto: Festus Osifo, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

TUC ta caccaki Tinubu kan karin albashi

Shugaban kungiyar, Festus Osifo ya bayyana haka a jiya Laraba 15 ga watan Mayu yayin hira da Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamred Osifo ya caccaki gwamnatin inda ya ce kwata-kwata ba ta shirya tattaunawa da ma'aikata ba.

Ya ce kananan ma'aikatan Gwamnatin Tarayya na karbar N77,000 a wata, gabatar da N48,000 abin takaici ne.

Albashi: TUC ta faɗi wahalar ma'aikatan Najeriya

"Kafin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bar mulki, karamin ma'aikaci a Gwamnatin Tarayya yana karbar N42,000 a wata."
"Idan aka hada da kudin rage radadi N35,000 da N42,000 kenan ma'aikaci karami yana samun N77,000 kenan."
"Tambaya a nan ita ce idan karamin ma'aikaci yana samun N77,000 meye dalilin gabatar N48,000 a matsayin mafi karancin albashi, wannan shiririta ne."

- Festus Osifo

Osifo ya kalubalanci gwamnatin ta kawo wani tsari da N48,000 zai isa ma'aikaci a wata ba tare da wata matsala ba.

Kara karanta wannan

'Ƴan ƙwadago sun yi fatali da mafi ƙarancin albashin da gwamnatin Tinubu ta gabatar

Tattaunawar Legit Hausa da wasu ma'aikata

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu ma'aikata kan gabatar da mafi karancin albashin N48,000 da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Ma'aikacin lafiya, Aliyu Dauda ya ce kudin ya yi kadan duba da halin da ake ciki na matsin rayuwa.

"Kwata-kwata kudin ya yi kadan, ya kamata a sake duba lamarin duk da naji za a sake sake zama kan mafi karancin albashi."

- Aliyu Dauda

Umar Abdulkadir da ke ma'aikatar SUBEB a Gombe ya ce babbar matsalar da ake samu shi ne ko da an tabbatar da hakan ba dole ma'aikatan jihohi su ci gajiya ba.

Ya koka kan yadda ake ta jan lokaci kan mafi karancin albashi duk da halin kunci da ake ciki a yanzu.

Kwadago ta yi fatali da albashin N48,000

A wani labarin, kungiyar kwadago ta yi Allah wadai da gabatar da N48,000 da Gwamnatin Tarayya ta yi a matsayin mafi karancin albashi.

Kara karanta wannan

"Akwai yiwuwar gwamnatin Tinubu ta kara kasafin 2024 domin gyara albashin ma'aikata," IMF

Kungiyar ta ce ba za ta taba amincewa da hakan ba ganin halin da ƴan kasar ke ciki a yanzu na tsadar kayayyaki musamman na abinci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.