Adadin Mutanen da Suka Mutu a Harin 'Bam' da Aka Kai Masallaci a Kano Ya Haura 5

Adadin Mutanen da Suka Mutu a Harin 'Bam' da Aka Kai Masallaci a Kano Ya Haura 5

  • Wasu ƙarin mutum bakwai daga cikin waɗanda suka samu rauni a harin masallaci a jihar Kano sun riga mu gidan gaskiya
  • Hakan ya sa adadin waɗanda suka mutu a harin ya zama mutum takwas yayin da sauran mutane 17 ke kwance a asibitin Murtala Muhammad
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna kiyawa ne ya bayyana haka ga manema labarai a Kano

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rahotanni daga jihar Kano sun nuna cewa adadin waɗanda suka mutu a harin masallacin da aka kai a ƙaramar hukumar Gezawa a Kano ya ƙaru.

Ƙarin mutum bakwai sun riga mu gidan gaskiya yayin da ake kokarin yi masu magani a asibitin Murtala Muhammad da ke birnin Kano.

Kara karanta wannan

"Abin da ya sa na ƙona mutane suna sallah a Kano," Wanda ake zargi ya faɗi gaskiya

Kwamishinan ƴan sandan Kano, CP Usaini Gumel.
Karin mutum bakwai sun riga mu gidan gaskiya sakamakon harin masallaci a Kano Hoto: Kano Police Command
Asali: Facebook

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, shi ne ya tabbatar da haka ga Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ƙarin mutum bakwai sun rasu ne sakamakon raunukan da suka samu a harin, wanda jimulla mutum takwas kenan suka rasa rayuwarsu.

A cewar kakakin ƴan sandan, a yanzun mutane 17 suka rage waɗanda ke kwance ana masu magani a asibitin.

Idan baku manta ba, Legit Hausa ta kawo muku rahoton yadda wani mutumi ya tashi abin da ake zargin bam ne a masallaci a kauyen Laraba Abasawa da ke yankin Gezawa.

Lamarin dai ya faru ne da misalin ƙarfe 5:20 yayin da mutane ke tsaka da Sallar Asubahi ranar Laraba, 15 ga watan Mayu, 2024.

Me ya haddasa kai harin a Kano?

Babban wanda ake zargi da aikata laifin, Shafi'u Abubakar, ɗan kimanin shekara 38 ya miƙa kansa ga rundunar ƴan sanda bayan faruwar lamarin, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wani mutum ya kone masallata su na tsakar sallar asubahi a Kano

Ya kuma shaidawa ƴan sanda cewa ya aikata wannan ɗanyen aikin ne saboda waɗanda yake zargin sun zalunce shi a rabon gadon gidansu su na cikin masallacin.

Sai dai tun da farko an tabbatar da mutuwar mutum ɗaya, wasu 24 kuma na kwance a asibiti, to amma yanzu ƙarin mutum bakwai sun kwanta dama.

Matsalar tsaro ta shiga Kano?

A wani rahoton gwamnatin Kano ta musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewa matsalar tsaro ta ɓulla a wasu sassan jihar da ke Arewa maso Yamma.

Mataimakin Gwamnan jihar, Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo ne ya musanta labarin a ranar Litinin, inda ya ce akwai rashin adalci a yada babu tsaro a Kano

Asali: Legit.ng

Online view pixel