Ana Tsoron Rikici kan Tukunyar Miya ya Janyo Asarar Rayuka a Birnin Abuja

Ana Tsoron Rikici kan Tukunyar Miya ya Janyo Asarar Rayuka a Birnin Abuja

  • Akalla mutane uku ne ake fargabar sun rasa rayukansu a wani rikici da ya kaure tsakanin baban bola da mutanen da ke zaune a Kubwa da a Abuja
  • Rigimar ta samo asali ne bayan an yi zargin wani baban bola da yunkurin dauke tukunyar wata mata mazauniyar unguwar Byazhin
  • Bayan ta nemi daukin makwabta ne aka dakile yunkurin baban bolan, shi kuma sai ya tattaro yan abokansa su ka dawo da makamai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Rikici ya kaure tsakanin wasu masu aikin baban bola da mutanen unguwar Byazhin da ke kauyen Kubwa a karamar hukumar Bwari da ke babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Majalisa ta amince gwamnati ta karbo bashin $500m a magance matsalar wuta

Rahotanni sun bayyana cewa akalla mutane uku ne ake fargabar sun rasa ransu a artabun.

Yan sanda
Ana fargabar rikici kan tukunyar miya ya janyo asarar rayuka a Abuja Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Leadership News ta wallafa cewa ana fargabar an kashe wasu mata biyu, da yaro guda yayin hatsaniyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abuja: Yadda rikicin ya samo asali

Tun da fari dai lamarin ya samo asali ne daga lokacin da wani baban bola ya yi yunkurin sungume tukunyar miyar wata mata.

The Sun ta tattaro cewa Jessica Adams ta ce a lokacin ne mai tukunyar ta nemi agajin makwabta da sauran ma su wucewa.

Nan ta ke su ka kawo mata dauki, inda su ka kwace tukunyar miyar gami da yiwa 'barawon' dukan tsiya.

Ta ce bayan baban bolan ya tafi ne sai ya gayyato abokansa, su ka shigo da adduna da sauran makamai su na sare-sare har aka kashe mutum uku, ciki har da mai tukunyar miyar.

Kara karanta wannan

"An yi amfani da bam": Mutum 1 ya mutu da aka bankawa masallata wuta a Kano

Matsayar 'yan sandan reshen Abuja

Rundunar 'yan sandan Abuja ta musanta cewa mutane uku sun mutu a yankin Byazhin da ke karamar hukumar Bwari sakamakon wani rikici.

Duk da ta tabbatar da afkuwar rikicin, kakakin rundunar SP Josephine Adeh ta ce an dai jikkata wasu, da a yanzu haka su ke karbar magani.

Ta bayyana cewa labarin rasa rai ba gaskiya ba ne, domin tuni jami'ansu su ka kwantar da tarzomar.

Fada ya kaure tsakanin garuruwa 2 a Neja

A baya mun ba ku labarin yadda rikici ya balle a kauyen Tswako Makun da na Gbangba Dzuko, a karamar hukumar Gbako da ke jihar Neja.

Asalin rikicin ya faro ne lokacin da wani matashi Gbangba Dzuko ya yi yunkurin sumbatar wata amarya ana tsaka da shagalin bikin aure.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel