Trump Ya Saki Baki, Ya Bayyana Abin da Zai Iya Faruwa a Zama na 2 tsakanin Amurka da Iran

Trump Ya Saki Baki, Ya Bayyana Abin da Zai Iya Faruwa a Zama na 2 tsakanin Amurka da Iran

  • Shugaba Donald Trump ya yi ikirarin cewa kasar Amurka da Iran za su cimma matsaya kuma su rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu a yau
  • Trump ya kuma sanar da cewa tawagar Amurka karkashin jagorancin mataimakinsa, JD Vance na kan hanyar zuwa birnin Islamabad
  • Wannan na zuwa ne yayin da Pakistan ke ci gaba kokarin sake hada kasashen biyu a teburin tattaunawa karo na biyu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

United States - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa ana sa ran rattaba hannu kan yarjejeniya da Iran a yau Litinin, 20 ga watan Afrilu, 2026.

Shugaba Trump ya kuma tabbatar da cewaa tawagar Amurka karkashin jagorancin mataimakinsa, JD Vance na kan hanyarta zuwa Islamabad domin zagaye na biyu na tattaunawa.

Shugaba Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana jawabi ga manema labarai kan yakin Iran Hoto: Tasos Katapolis
Source: Getty Images

Rahotannin da tashar Al-Jazeera ta tattaro sun nuna cewa an samu ƙarin ƙwarin gwiwa a Islamabad kan yiyuwar samun nasarar shirya tattaunawar sulhu a karo na biyu bayan gagarumin shiri da aka yi.

Kara karanta wannan

Yawan surutun shugaban Amurka, Trump ya jawo masa martani mai zafi daga kasar Iran

Tawagar Amurka na kan hanya

A wata hira da ya yi da New York Post, Trump ya ce mataimakin shugaban kasa, JD Vance, Steve Witkoff, Jared Kushner da sauran ‘yan tawagar Amurka suna kan hanyar zuwa Islamabad kuma za su isa cikin sa’o’i kaɗan masu zuwa.

Ya ƙara da cewa yana shirye ya gana da manyan shugabannin Iran idan aka samu ci gaba a tattaunawar da ake yi.

Trump ya jaddada cewa babban abin da Amurka ke nema wanda ba sai an tattauna a kansa b shi ne Iran ta daina kokarin mallakar makamin nukiliya

Shirin sulhu da Pakistan ke yi

A cewar majiyoyi, akwai kyakkyawan fata cewa zagaye na biyu na tattaunawar zai gudana, ganin yadda aka samu gagarumin ci gaba a baya.

An kuma rawaito cewa shugaban rundunar sojin Pakistan ya shafe kwanaki uku yana wajen ƙasar domin tabbatar da nasarar sasanci tsakanin ɓangarorin biyu.

Haka kuma, ministan harkokin cikin gida na Pakistan ya gana da jakadun Amurka da Iran, inda ya tabbatar musu da tsaro yayin tattaunawar.

Kara karanta wannan

Ana maganar sulhu, Trump ya yi barazanar sake sakin bama bamai a Iran

Islamabad.
Wurin da Pakistan ta shirya tattaunawar farko tsakanin Amurka da Iran a birnin Islamabad Hoto: Pool
Source: Getty Images

Mashigar Hormuz na iya kawo cikas

Jami’an Pakistan sun ce suna sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a mashigar ruwa ta Hormuz, wanda zai iya zama cikas ga samun zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran.

Duk da haka, komai zai ta’allaka ne kan yadda ɓangarorin biyu za su amince su koma teburin tattaunawa domin cimma matsaya.

Trump ya ce tawagar Amurka ta kama hanyar zuwa wurin tattaunawar kuma yana fatan za a rattaba hannu kan yarjejeniya a yau, amma Iran ta ce ba ta yanke shawarar tura tawagarta ba.

Iran na neman janyewa daga sulhu

A wani labarin, kun ji cewa Iran ta bayyana cewa har yanzu ba ta yanke shawarar ko za ta shiga zagaye na biyu na tattaunawa da Amurka ba.

Iran ta tuna yadda Amurka ta kai mata hare-hare a daidai lokacin da ake tsaka da tattaunawar diflomasiyya, tana mai cewa ba za ta taba manta wa da hakan ba.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei ya ce kasarsa ba za ta manta da yaudara biyu da Amurka ta mata ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262