Hukumar Hisbah Ta Saka Sabuwar Doka Kan Harkokin Biki a Jihar Kano

Hukumar Hisbah Ta Saka Sabuwar Doka Kan Harkokin Biki a Jihar Kano

  • Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta tattauna da masu aiki lura da saka sauti a wajen bukukuwa da aka fi sani da DJ
  • A yayin taron hukumar Hisbah ta sanar da sabuwar doka wacce za ta takaita cakuduwar maza da mata a lokacin biki
  • Shugaban masu aikin DJ na jihar Kano, Ibrahim Abdullahi ya bayyana yadda kungiyarsu ta karbi sabuwar dokar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da kafa sabuwar doka da ta shafi harkokin bukukuwa.

Daurawa
HIsbah ta gana da masu aikin DJ domin hana cakuduwar maza da mata a Kano. Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Asali: Facebook

Rahotanni sun nuna cewa dokar ta shafi hana maza ma su lura da saka sauti a wuraren taro da aka fi sani da DJ aiki a bukukuwan mata.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta dakatar da wata likita saboda barin mara lafiya a bakin mutuwa

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa babban kwamandan Hisba na jihar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bada sanarwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daurawa ya fadi dalilin kafa dokar DJ

Malam Daurawa ya ce manufar dokar shine tsaftace jihar kan cakuduwar maza da mata ba bisa ka'ida ba.

A matsayin jihar da ake aiki da Shari'a, Daurawa ya ce bai dace a bar maza da mata na cakuduwa ba.

Saboda ana ganin hakan hanya ce da za ta kawo yaɗuwar fasikanci a cikin al'ummar jihar Kano, rahoton jaridar Tribune.

Sai kuma ya kara da cewa daga yanzu mata masu aikin DJ ne za su rika gudanar da hidimar bukukuwan mata ƴan uwansu.

Hisbah ta zauna da masu wuraren taro

Bayan haka malamin ya kara da cewa hukumar ta zauna da masu wuraren taro na jihar domin musu karin haske kan dokokin Hisbah.

Kara karanta wannan

Operation kauda badala: Hisbah ta damke maza da mata 20 suna wanka tare a Kano

Wannan duk kokari ne na kawo gyara da hukumar ke yi a kan lamuran bukukuwa domin tabbatar da tarbiyyar al'umma.

Hisbah: Jawabin kungiyar masu aikin DJ

A nasu bangaren, masu aikin DJ a jihar sun nuna godiya bisa gayyatar da Hisba ta musu da kuma bayyana musu yadda aikin zai cigaba da gudana.

Shugabansu na jihar Kano, Ibrahim Abdullahi ya ce za su yi kokari wajen tabbatar da cewa sun yi aiki da dokar.

Za a sake auren zawarawa a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa Hukumar Hisba ta jihar Kano ta fara shirye shiryen auren zawarawa karo na biyu tun bayan hawan mulkin Abba Kabir Yusuf.

Kwamandan rundunar ne, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana lamarin yayin hira da manema labarai tare da karin haske kan yadda auren zai gudana a wannan karon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel