Sanata Shehu Sani Ya Bayyana Yadda Suka Sha Azaba Tare da Obasanjo a Gidan Yari

Sanata Shehu Sani Ya Bayyana Yadda Suka Sha Azaba Tare da Obasanjo a Gidan Yari

  • Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda suka sha wahala tare da tsohon shugaban kasar Najeriya cif Olusegun Obasanjo a gidan yari
  • A shekarar 1995 ne aka yanke wa Sanata Shehu Sani hukuncin daurin rai da rai a gidan yari da ke Kirikiri a jihar Legas bisa cin amanar kasa
  • An yankewa tsohon shugaban kasar Najeriya, cif Olusegun Obasanjo hukuncin daurin rai da rai ne bisa kitsa juyin mulki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya ya bayyana yadda suka sha bakar wahala a gidan yari.

Shehu sani Obj
Shehu Sani ya ce sun sha wahala lokacin da suka zauna a gidan yarin Legas. Hoto: Senator Shehu Sani, Gabriel Aponte
Asali: UGC

Sanata Shehu Sani ya bayyana lamarin ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a jiya Laraba, 15 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Aiki ba lasisi: Kotu ta yanke hukuncin dauri kan 'yan canji 17 da aka kama a Kano

A cewar Sanatan, a lokacin da suke gidan yarin, ma'aikata sun azabtar da shi tare da tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe aka kama Shehu Sani?

A lokacin mulkin Janar Sani Abacha ne Sanatan da tsohon shugaban kasar suka samu kansu a gidan yarin Kirikiri da ke jihar Lagos.

Sanatan ya nuna jarunta lokacin da kowa ke tsoron magana kan gwamnatin soja wanda hakan har sai da ya kai ga yanke masa hukuncin daurin rai da rai.

Wadanda aka daure tare da Shehu Sani

Gidan yarin ya cika da manyan yan siyasa a wancan lokacin ciki har da Ken Saro-Wiwa da Janar Shehu Musa Yar'adua.

Sai dai an rataye Ken Saro-Wiwa ne daga baya shi kuma Shehu Musa Yar'adua ya rasu a gidan yarin.

Duk da Sanatan da tsohon shugaban kasar ba su yi tsammanin fita daga gidan yarin ba, cikin ikon Allah sun fito daga baya.

Kara karanta wannan

Kano: Sanata Hanga ya yi karin haske kan dalilin rabon kayan gawa a makabartu

Sakon da Shehu Sani ya wallafa

A cikin sakon da Sanata Shehu Sani ya wallafa a shafin X ya haɗa da hotonsa da na tsohon shugaban kasar bayan sun fita daga gidan yarin. Ga abin da yake cewa:

"Wannan hoton yana tuna mani lokacin da nake tsokana da tunawa tsohon shugaban kasa, Obasanjo yadda aka ba mu kashi a gidan yarin Kirikiri a shekarar 1995"

Obasanjo ya koka kan tsarin mulki

A wani rahoton, kun ji cewa wasu yan majalisar wakilan Najeriya sun fara yunkurin kawo sauyi a tsarin mulkin da ake bi a tarayyar Najeriya.

Yan majalisar sun kai ziyara ga tsohon shugaban kasa Obasanjo domin neman goyon baya kan sabon aikin da suka dauka na canja tsarin mulkin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel