Bola Tinubu Ya Gana da Gwamna Ahmed Ododo a Villa, Sun Tattauna Batutuwa da Dama

Bola Tinubu Ya Gana da Gwamna Ahmed Ododo a Villa, Sun Tattauna Batutuwa da Dama

  • Bola Ahmed Tinubu ya gana da Gwsmna Ahmed Usman Odo a fadar shugaban ƙasa da ke birnin Abuja ranar Laraba, 15 ga watan Mayu
  • Gwamna Ododo ya ziyarci Tinubu ne domin yi masa ƙarin bayani kan yanayin tsaro a jihar Kogi musamman bayan abin da ya faru
  • A ƴan kwanakin nan ne wasu ƴan bindiga suka shiga jami'a suka sace ɗalibai a Kogi amma jami'an tsaro sun ceto ɗaliban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya karɓi bakuncin Gwamna Ahmed Usman Ododo na jihar Kogi a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Laraba.

Gwamna Ahmed Ododo ya ziyarci Bola Tinubu ne domin yi masa bayani kan abubuwan da suka faru kwanan nan a jihar Kogi.

Kara karanta wannan

"Abin da ya sa na ƙona mutane suna sallah a Kano," Wanda ake zargi ya faɗi gaskiya

Tinubu da Ahmed Ododo.
Bola Ahmed Tinubu ya karɓi bakuncin gwamnan jihar Kogi a Villa Hoto: @KingsleyFanwo
Asali: Twitter

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya wallafa a manhajar X ranar Laraba, 15 ga watan Mayu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin zaman, Shugaban Ƙasa Tinubu ya nuna gamsuwa da goyon baya kan yadda Gwamna Ododo ke tafiyar da harkokin tsaro a jihar da ke Arewa ta Tsakiya.

A nasa ɓangaren, Gwamna Ahmed Ododo ya tabbatar da cewa ganawarsa da shuugaban ƙasa ta yi kyau kuma sun tattauna batutuwa da dama.

Gwamna Ododo da Tinubu sun tattauna batutuwa

Bugu da ƙari, kwamishinan yaɗa labarai, Fanwo ya ce taron manyan shugabannin biyu ya taɓo wasu ɓangarori da suka shafi inganta rayuwar talakawa.

Mista Fanwo ya ce a tattunawar da Tinubu ya yi da Ododo, sun taɓo harkokin ilimi, jin daɗi da walwalar ma'aikata, kiwon lafiya da sauran batutuwa masu muhimmanci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu na tunanin kwashe kuɗin ƴan fansho ta yi wasu muhimman ayyuka

Gwamna Ahmed Ododo ya kuma tattauna batun yadda za a magance rikicin da ya ɓalle a ƙaramar hukumar Omala a lokacin ganawarsa da Shugaba Tinubu.

Wannan na zuwa ne bayan harin da ƴan bindiga suka kai hari jami'ar kimiyya da fasaha a jihar Kogi, inda suka tafi da ɗalibai da dama.

Bayan faruwar haka ne gwamnan ya haɗa runduna ciki har da mafarautan da suka san yankin suka bi sawun ƴan bindigar kuma suka ceto ɗaliban.

NLC da TUC sun yi watsi da N48,000

Wani rahoton kuma Ƙungiyoyin ma'aikata a Najeriya sun yi fatali da sabon mafi ƙarancin albashi wanda gwamnatin tarayya ta gabatar masu yau Laraba.

Gwamnatin ta ba da shawarar a ƙara mafi ƙarancin albashin daga N30,000 zuwa N48,000 a taron kwamitin da aka kafa a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel