Gwamna a Najeriya Ya Tafka Babban Rashin Jigo a Gwamnatinsa, Ya Kaɗu Matuƙa

Gwamna a Najeriya Ya Tafka Babban Rashin Jigo a Gwamnatinsa, Ya Kaɗu Matuƙa

  • Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya sanar da mutuwar mataimakin shugaban ma'aikatansa, Gboyega Soyannwo
  • Sanwo-Olu ya bayyana rasuwar marigayin ne a yau Laraba 15 ga watan Mayu a shafinsa na X inda ya ce ya kadu da rasuwar
  • Gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin dan uwa ba wai ma'aikaci ba inda ya yi masa addu'ar samun rahama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Mataimakin shugaban ma'aikatan gwamnan jihar Legas, Gboyega Soyannwo ya kwanta dama.

Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu shi ya tabbatar da mutuwar na hannun damansa a yau Laraba 15 ga watan Mayu.

Gwamnan Lagos ya tafka babban rashi a gwamnatinsa
Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Lagos ya sanar da mutuwar mataimakin shugaban ma'aikatansa, Gboyega Soyannwo. Hoto: @jidesanwoolu.
Asali: Twitter

Gwamna Sanwo-Olu ya kadu da mutuwar Gboyega

Kara karanta wannan

Yayin da ake kukan tsadar kujerar hajji, Tinubu ya tausaya da tallafin biliyoyi

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, Gbenga Omotosho ya fitar a yau Laraba 15 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Omotosho ya ce Soyannwo ya mutu ne a yau Laraba 15 ga watan Mayu bayan fama da jinya yana da shekaru 55 a duniya.

A cikin wata wallafa da gwamnan ya yi a shafinsa na X ya ce kadu da mutuwar mataimakin shugaban ma'aikatansa.

"Ina mai bakin cikin sanar da mutuwar mataimakin shugaban ma'aikatana, Gboyega Soyannwo."
"Na kadu matuka da wannan mutuwa ta Gboyega da ta zo a bazata, wannan labari ya rikita ni."

- Babajide Sanwo-Olu

Lagos: Matsayin Gboyega a wurin Sanwo-Olu

Sanwo-Olu ya ce Gboyega ya kasance kamar ɗan uwa a gare shi ba wai mataimakin shugaban ma'aikatansa ba.

Ya ce gudunmawar da Gboyega ya bayar ba za a taba mantawa da ita ba a Lagos inda ya jajantawa iyalansa da ƴaƴansa kan wannan babbar rashi.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Fubara ya ga ta kansa yayin da kwamishinoni 2 suka ajiye aiki

Zulum ya tafka babbar rashi

Kun ji cewa Gwamna Babagana Umara Zulum ya rasa hadiminsa, Cif Kester Ogualili a birnin Maiduguri da ke jihar Borno.

Ogualili ya rasu ne a ranar 4 ga watan Mayun wannan shekara a asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri bayan fama da jinya.

Marigayin wanda ya fito daga karamar hukumar Dunukofia a jihar Anambra ya shafe mafi yawan rayuwarsa a Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.