'Zai Babbake Iran': Yadda Babban Soja Ya 'Hana' Trump Amfani da Nukiliyar Amurka

'Zai Babbake Iran': Yadda Babban Soja Ya 'Hana' Trump Amfani da Nukiliyar Amurka

  • Rahotanni sun bayyana cewa wani babban soja a Amurka ya dakile yunkurin Donald Trump na amfani da nukiliya
  • Majiyoyi suka ce Donald Trump ya nemi amfani da lambobin nukiliya yayin taron gaggawa, amma aka hana shi
  • Wani tsohon jami’in CIA Larry Johnson ya bayyana cewa an samu takaddama mai zafi a Fadar White House yayin da aka hana Trump damar samun lambobin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - An samu taƙaddama a fadar White House yayin taron gaggawa da Shugaba Donald Trump.

Rahotanni sun nuna cewa shugaba Trump ya kasa samun damar amfani da lambobin nukiliya na ƙasar bayan wani babban jami’in soja ya hana shi.

An hana Trump amfani da lambobin sirrin nukiliyar Amurka
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana jawabi ga manema labarai kan yakin Iran Hoto: Tasos Katapolis.
Source: Getty Images

An hana Trump amfani da lambobin sirrin nukiliya

Rahoton The Mirror ya ce wannan bayani ya fito daga wani tsohon jami’in CIA mai suna Larry Johnson kan yunkurin Trump na amfani da nukiliyar.

Kara karanta wannan

"Saura ƙiris": Trump ya faɗi lokacin kawo ƙarshen yaƙi da Iran

A cewar Johnson, lamarin ya faru ne a yayin wani taron gaggawa da aka gudanar a Fadar White House da ke Washington.

Ya ce Trump ya yi ƙoƙarin neman lambobin nukiliya, amma babban hafsan soji Janar Dan Caine ya tsaya tsayin daka ya ce “a’a,” lamarin da ya haifar da takaddama mai zafi.

Sai dai rahoton bai samu cikakken tabbaci daga hukumomi ba, kuma har yanzu ba a san dalilin da yasa Trump zai bukaci lambobin nukiliya a wannan lokaci ba.

An yi taƙaddama da Trump yayin taro a Washington
Shugaban Amurka, Donald Trump jim kadan bayan jawabi ga 'yan majalisar Republican a Doral, Florida. Hoto: Roberto Schmidt.
Source: Getty Images

Taƙaddamar da aka samu a fadar White House

Rahotanni sun kuma bayyana cewa bayan an harbo wani jirgin yakin Amurka da Iran ta yi, Trump ya shafe sa’o’i yana yi wa ma’aikata ihu a cikin White House, yana tuna abubuwan da suka faru a rikicin garkuwa da mutane na Iran a shekarar 1979.

Wannan na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun ce an hana Trump shiga wani dakin taro yayin wani muhimmin aikin ceto da ya shafi Iran.

Ana zargin cewa jami’an tsaro sun dauki matakin ne saboda tsoron yadda halayensa ka iya shafar aikin, cewar France24.

Kara karanta wannan

Ana shirin sake zama, Trump ya fadi abin da zai harzuka Jamhuriyar Musulunci ta Iran

Tun daga ranar 28 ga Fabrairun 2026, Amurka da Isra’ila suka kai hare-hare kan wasu muhimman wurare a Iran, lamarin da ya jawo martani daga Iran ta hanyar kai hare-hare.

Haka kuma, an rufe muhimmin mashigin ruwa na Strait of Hormuz, wanda ke da matukar tasiri ga harkokin kasuwancin mai a duniya.

Duk da cewa an samu tsagaita wuta na wucin gadi, har yanzu ba a cimma yarjejeniyar zaman lafiya ba.

A halin yanzu, ana ci gaba da fargaba kan yiwuwar sake barkewar rikici, yayin da tattaunawar zaman lafiya ke ci gaba da kasancewa cikin shakku.

Trump ya sake magana kan tattaunawa da Iran

A wani labarin, mun ba ku rahoto cewa shugaba Donald Trump ya yi ikirarin cewa kasar Amurka da Iran za su cimma matsaya kuma su rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu a yau.

Trump ya kuma sanar da cewa tawagar Amurka karkashin jagorancin mataimakinsa, JD Vance na kan hanyar zuwa birnin Islamabad.

Wannan na zuwa ne yayin da Pakistan ke ci gaba kokarin sake hada kasashen biyu a teburin tattaunawa karo na biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.