"Babu Ja da Baya": Limaman Musulunci Sun Ɗaga Yatsa Ga Ministar Tinubu Kan Aurar da Mata 100

"Babu Ja da Baya": Limaman Musulunci Sun Ɗaga Yatsa Ga Ministar Tinubu Kan Aurar da Mata 100

  • Yayin da aka dakatar da shirin aurar da mata marayu a Niger, limaman Musulunci sun sha alwashin ci gaba da shirinsu kan lamarin
  • Kungiyar limaman ta ce babu mai hana aurar da matan inda ta kalubanci Ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye kan matakin da ta ɗauka
  • Hakan ya biyo bayan maka kakakin Majalisar jihar da Uku ta yi a kotu kan shirin aurar da mata marayu 100 a karamar hukumar Mariga

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Nijar - Kungiyar limaman Musulunci a jihar Niger sun sha alwashin aurar da mata marayu 100 da aka yi niyya.

Limaman da sauran kungiyoyin addini sun yi fatali da korafin Ministar harkokin mata kan shirin aurar da yaran a karamar hukumar Mariga.

Kara karanta wannan

Bulaliyar kan hanya: Tinubu, Shettima za su fara biyan harajin fakin a filin jirgin sama

Malaman Musulunci sun kalubalanci Minista kan aurar da mata 100 a Niger
Limaman Musulunci sun sha alwashin ci gaba da shirin aurar da mata 100 a jihar Niger. Hoto: Uju Kennedy-Ohanenye, Abdulmalik Sarkin-Daji.
Asali: Facebook

Sarkin-Daji zai aurar da mata 100

Hakan ya biyo bayan alkwarin da kakakin Majalisar jihar, Abdulmalik Sarkin-Daji ya yi na daukar nauyin aurar da mata marayu, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani, Ministar harkokin mata, Uku Kennedy-Ohanenye ta kalubalanci Sarkin-Daji inda ta maka shi a kotu.

Bayan matakin da Ministar ta dauka, sai kakakin Majalisar ya janye kudurinsa kan shirin da ya yi niyya a jihar na aurar da matan, cewar rahoton Punch.

Aure: Malaman Musulunci sun bijirewa Minista

Malaman suka ce za su ci gaba da shirin aurar da matan tun da bai saba kundin tsarin mulki ba da kuma addinin Musulunci.

Daraktan hukumar harkokin addini a jihar, Dakta Umar Farouk shi ya bayyana haka a yau Laraba 15 ga watan Mayu a birnin Minna.

Farouk ya ce babu abin da zai hana su aiwatar da shirin inda ya ba Ministar wa'adin kwanaki bakwai da ta janye karar da ta shigar.

Kara karanta wannan

Ministar Tinubu ta maka kakakin Majalisa a kotu kan shirin aurar da mata marayu 100

Ya ce idan kuma ba ta janye karar kakakin Majalisar da ta yi ba, to ita ma za ta fuskanci shari'a a kotu.

Ya bukaci ta ba al'ummar Niger hakuri da kakakin Majalisar kan bata suna inda ya bukaci Bola Tinubu ya kore ta saboda neman kawo rikicin addini a kasar

Za a aurar da mata marayu 100

Kin ji cewa kakakin majalisar jihar Niger, Abdulmalik Sarkin-Daji ya dauki nauyin aurar da mata marayu 100 a mazabarsa.

Rt. Ho. Sarkin-Daji ya yi wannan alkawari ne inda ya ce hakan zai tallafa musu bayan kisan iyayensu da ƴan bindiga suka yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.