Sojojin Najeriya Sun Kama Rijiyoyin Mai na Bogi a Jihar Ribas

Sojojin Najeriya Sun Kama Rijiyoyin Mai na Bogi a Jihar Ribas

  • Rundunar sojin Najeriya ta 6 da ke jihar Ribas sun yi nasarar kama barayin danyen mai a yankin Odagwa da ke karamar hukumar Etche
  • Laftanal Kanal Ishaya Manga ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da rundunar ta shirya domin nuna aikin da barayin suka yi
  • Rundunar sojin ta mika godiya ta musamman ga mutanen yankin bisa hadin kai da suke ba su wajen yaki da miyagu ba dare ba rana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

jihar Ribas - Rundunar sojin Najeriya sun gano rijiyoyin mai biyar da barayin danyen mai suka haka a jihar Ribas.

Barayin mai
Sojoji sun gano gidajen da ake sarrafa danyen mai a Ribas. Getty Images
Asali: Getty Images

Sojojin sun sanar da kama masu satar danyen man ne da litar mai 45,000 a yau Laraba, 15 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Ana tsoron rikici kan tukunyar miya ya jawo asarar rayuka a birnin Abuja

Rahoton da jaridar Daily Trust ta fitar ya nuna cewa lamarin ya faru ne a yankin Odagwa da ke karamar hukumar Etche.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barayin mai: Jawabin dakarun sojojin Najeriya

Da yake jawabi a madadin kwamandan rundunar, Laftanal Kanal Ishaya Manga ya ce barayin danyen man suna amfani ne da tukwane wurin tace shi.

Laftanal Kanal Ishaya Manga ya kara da cewa nasarar da suka samu ta samo asali ne daga farautar barayin da suka fara tun watan Fabrairu.

Ya tabbatar wa yan jarida cewa akwai wasu ramukan da bata garin suke cigaba da boye danyen mai a ciki amma sannu a hankali rundunar za ta cimma musu.

Rundunar soja ta godewa mutanen yankin

Laftanal Kanal Ishaya Manga ya yi godiya ga mutanen yankin kan cigaba da goyon baya da suke basu wurin yaki da barayin, rahoton Platform Times.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa ya tsananta, Izala ta umarci masallatai a fara Al-kunut

Sannan ya kara rokon al'ummar da su cigaba da ba jami'an tsaron Najeriya hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya da cigaba.

Sojoji sun kama barayin danyen mai

A wani rahoton, kun ji cewa sojoji sun ci karo da wani wuri da aka haka ramuka masu matsakaitan zurfi domin a rika satar danyen man Najeriya.

Abin da ya ba kowa mamaki shi ne an ci karo da mai a wadannan ramuka, kuma tsageru suna yin abin da suka ga dama ba dare ba rana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng