Nazari: Yadda Mutane 1500 a Majalisun Tarayya da Jihohi Za Su Cinye N724bn a Shekarar 2024

Nazari: Yadda Mutane 1500 a Majalisun Tarayya da Jihohi Za Su Cinye N724bn a Shekarar 2024

Abuja - Majalisar dokokin tarayya da majalisun jihohi 36 tare da hukumomin da ke karkashin su za su kashe kimanin N720bn a bana, kamar yadda kasafinsu na 2024 ya nuna.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Wani bincike ya kuma nuna cewa albashi da alawus na ‘yan majalisar tarayya da na jihohi zai lakume kusan N50bn a bana.

Hakan na nufin gwamnatin tarayya da na Jihohi sun ware Naira biliyan 673.94 ga majalisun kasa da na jihohi da kuma hukumomin da ke da alaka da su a cikin kasafin 2024.

Albashin 'yan majalisar tarayya da na jihohi
Yadda gwamnati za ta kashe N724bn wajen biyan albashi da alawus din 'yan majalisar tarayya da na Jihohi. Hoto: @nassnigeria
Asali: Twitter

An tattara bayanai na albashi da alawus na 'yan majalisun daga wata takardar da aka samu daga shafin yanar gizon hukumar tattara kudade da rarraba kasafim kuɗi.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da binciken TETFund, an fitar da N1bn a sharewa dalibai hawaye a makarantu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da haka, gabaɗayan alawus ɗin sun zarce adadin da aka bayar saboda ba a bayyana adadin alawus din da yawa daga cikin 'yan majalisar ba, jaridar The Punch ta ruwaito.

Albashin 'yan majalisar dattawa

Wani bincike ya nuna cewa ‘yan majalisar dattawa 109 za su samu N8.67bn a matsayin albashi da alawus alawus a wannan shekarar.

Shugaban majalisar dattawa zai karbi albashin N2.48m da alawus din N33.29m a shekara, yayin da mataimakin shugaban majalisar zai karbi albashin N2.31m da alawus din N30.94m.

Kowanne sanata ya na samun N2.03m a matsayin albashi a shekara sannan kuma ya na samun jimillar alawus na N72,137,440.

A bangaren albashi da alawus-alawus na wasu sanatoci, daga cikin alawus-alawus 20 da aka ambata, 15 ne kawai aka bayyana kudin da ake biyansu.

Albashin 'yan majalisar wakilai

A bangaren majalisar wakilai kuwa, kakakin majalisar na samun albashin N2.48m da alawus din N18.33m a shekara, yayin da mataimakinsa yake samun N2.29m matsayin albashi da alawus din N17.16m.

Kara karanta wannan

"Akwai yiwuwar gwamnatin Tinubu ta kara kasafin 2024 domin gyara albashin ma'aikata," IMF

Sauran ‘yan majalisar wakilai na samun N1.99m kowannen su a matsayin albashi a shekara, yayin da kowanne kuma ya ke samun N58.76m a matsayin alawus.

The BusinessNG ta ruwaito albashin ‘yan majalisar wakilai 358 ya kai jimillar N2.84bn yayin da alawus-alawus din su ya kai N21.04bn.

Albashin 'yan majalisar jihohi

Kakakin majalisar dokokin jiha na karbar albashin N1.64m da alawus din N5.58m a shekara, yayin da mataimakin kakakin majalisar ke samun N1.45m da alawus din N4.92m.

A jimlace, kakakin majalisa na jihohi 36 za su samu kusan N59.04m a matsayin albashi a shekara yayin da za a ba mataimakansu 36 albashin kusan N52.1m.

A dunkule, alawus alawus din masu 'yan majalisar jihohi 36 da mataimakansu zai ci N1.51bn.

Akwai mambobi 784 a majalisar dokokin jihohi 36, kowannensu yana karbar albashin N1.34m a shekara da alawus na N12.97m kowanne.

A jimlace, gwamnatin jihohi 36 na kashe kimanin N4.19bn a albashin mambobi 784 sannan ana biyan N10.17bn a matsayin alawus.

Kara karanta wannan

Kayayyaki za su kara tsada a Najeriya, an kara harajin shigo da kayan kasar waje

'Yan majalisar YPP sun koma LP

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan majalisar YPP da jam'iyyar ta dakatar da su a jihar Abia, sun sauya sheka zuwa jam'iyyar Labour mai mulki a jihar.

'Yan majalisar, Hon. Iheanacho Nwogu da Hon. Fyne Ahuama sun sauya shekar tare da yakin cewa jam'iyyar LP za ta yi masu adalci a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.