Jigawa: Kwanaki 6 da Mutuwarsa, INEC Ta Dauki Mataki Kan Kujerar 'Dan Majalisa

Jigawa: Kwanaki 6 da Mutuwarsa, INEC Ta Dauki Mataki Kan Kujerar 'Dan Majalisa

  • Kwanaki shida da mutuwar ɗan Majalisar Tarayya a jihar Jigawa, hukumar INEC ya ce babu kowa a kujerar
  • Hukumar ta dauki wannan mataki ne bayan mutuwar Hon. Isa Dogonyaro domin shirye-shiryen sake zaben cike gurbi
  • Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu shi ya tabbatar da haka a jiya Laraba 15 ga watan Mayu inda ya lissafo sauran mazabu a jihohi uku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta ce babu kujerar marigayi ɗan Majalisar Tarayya daga jihar Jigawa.

Hukumar ta ce za ta saka ranar sake zaɓen bayan mutuwar Hon. Isa Dogonyaro a ranar Juma'a 10 ga watan Mayu a Abuja.

Kara karanta wannan

Yayin da ake kukan tsadar kujerar hajji, Tinubu ya tausaya da tallafin biliyoyi

INEC ta fara shirye-shiryen gudanar da zabe bayan mutuwar ɗan Majalisa, Dogonyaro a Jigawa
Hukumar INEC ta ayyana kujerar dan Majalisa, Isa Dogonyaro daga Jigawa babu kowa. Hoto: Isa Dogonyaro, House of Representatives.
Asali: Facebook

INEC za ta shirya zaben cike gurbi

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu shi ya sanar da haka a jiya Laraba 15 ga watan Mayu a Abuja, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin kafin rasuwarsa, ya wakilci mazabar Garki/Babura a jihar Jigawa a Majalisar Wakilai.

Farfesa Yakubu ya kuma sanar da karin wasu mazabu a jihohi uku sanadin mutuwa ko kuma murabus na masu rike da kujerun.

Sauran mazabu da INEC za tayi zaɓe

Mazabun sun hada da mazabar Khana 2 a jihar Rivers da Bagwai/Shanono a jihar Kano sai kuma mazabar Zaria Kewaye a jihar Kaduna.

Yakubu ya ce da zaran hukumar ta kammala shirye-shirye za ta sanar da lokacin gudanar da zaben a wadannan mazabu.

Ya ce nan ba da jimawa ba hukumar za ta yi martani kan sahihancin zaben ƙananan hukumomi da kansiloli a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Bulaliyar kan hanya: Tinubu, Shettima za su fara biyan harajin fakin a filin jirgin sama

Dan Majalisar Jigawa, Dogonyaro ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabun Garki da Babura a jihar Jigawa, Isa Dogonyaro ya rasu.

'Dan Majalisar ya rasu ne a ranar Jumu'ah da ta gabata 10 ga watan Mayu a Abuja bayan gajeruwar jinya da ya yi fama da ita.

Yar uwarsa mai suna Amina Dogonyaro ita ta sanar da rasuwar a shafinta na Facebook tare da bayyana cewa za a masa sallah a masallacin kasa da ke Abuja bayan sallar Juma'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel