Latest
Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta musants rahotannin da ke yawo kan cewa ta nada mukaddashin hafsan sojin kasa. DHQ ta ce ko kadan ba ta yi wannan nadin ba.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi kalaman yabo ga Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir a yayin da ya ke mika masa sandar mulki a ranar Lahadi.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Apkabio ya tabbatarwa yan kasar nan cewa ba a gwamnatin Bola Tinubu aka fara samun matsalar tattalin arziki ba
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara ta farko fadar gwamnatin Jigawa. Sanusi II ya ce Kano da Jigawa duk abu daya ne. Sanusi II ya yabi ayyukan Umar Namadi
Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya bukaci matasan Najeriya da su shigo a rika damawa da su a harkokin siyasa. Ya ce bai kamata su gujewa neman mulki ba.
Adadin mutanen da suka mutu a fashewar tankar mai da ta afku a garin majiya, karamar hukumar Taura ta jihar Jigawa ya kai 180. Mazauna garin sun yi karin bayani.
Abba Kabir Yusuf ya taya Rabi'u Kwankwaso murnar ranar haihuwa. Kwankwaso ya cika shekaru 68 da haihuwa a duniya. Abba ya shafe shekaru 38 tare da Rabi'u Kwankwaso.
An nada Abdulsalami Bagudu a matsayin mukaddashin babban hafsan soji yayin da Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ke samun hutu. Rundunar ta yi karin bayani.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun tare babban titin hanyar Funtua zuwa Gusau a jihar Zamfara. Tsagerun sun kashe muum biyu tare da yin garkuwa mutane masu yawa.
Masu zafi
Samu kari