Za a Yi Fadan cikin Gida a Kotu, Gwamnati Ta Kai Shugaban Kwastam Kara gaban Alkali

Za a Yi Fadan cikin Gida a Kotu, Gwamnati Ta Kai Shugaban Kwastam Kara gaban Alkali

  • Hukumar Kula da Daidaito a Rabon Mukaman Gwamnatin Tarayya (FCC) ta shigar da kara kan Hukumar Kwastam
  • FCC na zargin hukumar kwastam da shugabanta, Bashir Adewale Adeniyi da kin bayar da bayanan daukar ma'aikata
  • Haka kuma, hukumar ta yi zargin cewa an yin biris da umarnin tsaida daukar ma'aikata da horar da wadanda aka dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Hukumar Kula da Daidaito a Rabon Mukaman Gwamnatin Tarayya (FCC) ta shigar da karar Shugaban hukumar kwastam kotu a Najeriya.

FCC ta gabatar da kara mai tuhuma guda hudu a kan Hukumar Kwastam da Shugabanta, Bashir Adewale Adeniyi bisa zargin karya dokokin aiki.

Kwastam
Shugaban Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi lokacin da aka kara masa matsayi a Abuja Hoto: @Opetuyii/x
Source: Twitter

An yi karar hukumar kwastam a kotu

Ranar Juma’a The Cable ta rahoto ana zarginsu da watsi daidaito wajen rabon mukaman gwamnati a yayin daukar ma'aikata na shekarar 2025/2026.

Kara karanta wannan

Amnesty ta bukaci a kama 'yan daban da suka kai wa Pantami hari a Gombe

An shigar da karar ne a ranar Alhamis 12 ga watan Nuwamba 2026 a babbar kotun tarayya da ke Abuja, kamar yadda takardar karar suka nuna mana.

Hukumar FCC ta zargi Kwastam da kin mika mata bayanan daukar sababbin ma'aikata, lamarin da ya hana ta sa ido kan yadda aka gudanar da aikin.

FCC mai kokarin ganin an yi adalci ta kuma zargi hukumar da watsi da umarnin da ta bayar na dakatar da daukar ma'aikatan da fara horar da su.

Sahara Reporters ta ce an dogara da sashe na 14(3) na dokar kafa Hukumar FCC ta shekarar 2004 wajen shigar da wannan kara a babbar kotun tarayyar.

Tuhume-tuhumen da FCC ta ke yi wa kwastam

A tuhuma ta farko, hukumar ta ce kwastam ta gaza mika mata jerin sunayen ma'aikatan da ta dauka a 2025, duk da cewa ta bukaci hakan tun watan Maris.

Haka kuma, FCC ta zargi Bashir Adeniyi da sakaci ko kuma yarda da yadda hukumar da yake jagoranta ta yi biris da bukatar da aka gabatar mata.

Kara karanta wannan

Yadda aka shigo da tarin makamai Najeriya ana shirin zaben 2027

A tuhuma ta biyu, FCC ta zargi kwastam da shugabanta da kin amsa gayyatar ta ko kuma mika kansu domin ta sa ido a aikin da aka dauka kwanan nan.

Sannan an tuhumi wadanda ake karar da ci gaba da daukar ma'aikata da horar da su duk da cewa sun samu wasikar dakatarwa tun ranar 23 ga Oktoba, 2026.

FCC ta ce hukumar ta yi biris da wannan umarni, sannan ta kasa kiyaye muhimman bayanan daukar ma'aikatan da kuma ba ta damar lura da lamarin.

Zargi na hudu kuwa shi ne kin samar da cikakkun ka'idojin cancanta da kuma sharuddan daukar ma'aikata alhali tun farkon shekara aka neman bayanin.

Hukumar ta ce rashin wadannan bayanai ya hana ta tantance yadda aka raba guraben aikin da ake da su tsakanin jihohin Najeriya da kuma shiyyoyin kasar.

Shugaban Kwastam
Shugaban Kwastam na Najeriya, Bashir Adewale Adeniyi Hoto: @NTANewsNow
Source: Twitter

Gwamna yana so a canza kwamishinan 'yan sanda

An ji labari cewa ana zargin Gwamna Abba Kabir Yusuf yana so a tura masa sabon kwamishinan ’yan Sanda da DPO da suke tare da shi gabanin zaɓe.

Idan labarin gaskiya ne, an samu rashin jituwa tsakanin gwamnan da hukumar ƴan sandan kan batun sauya wasu jami'ai da aka yi har maganar ta yi nisa.

Har zuwa yanzu ba a ji cewa babu daidaito tsakanin Abba Kabir Yusuf da CP Ibrahim Bakori PhD ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng