Tashin Hankali: An Kai Hari Wurin Taron Magoya bayan Peter Obi da Kwankwaso
- Wasu ’yan daba dauke da adduna, sanduna da duwatsu sun kai hari kan magoya bayan NDC yayin taron jama’a a Oregun, Jihar Legas
- Rahoto ya nuna cewa maharan sun tarwatsa taron tare da tilasta wa mutane tserewa domin tsira da rayukansu
- Harin ya faru ne da misalin karfe 11 na safe, bayan an fara taron cikin kwanciyar hankali a jihar Legas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Legas, Nigeria - Wasu ’yan daba sun kai hari kan magoya bayan jam’iyyar NDC a yau Alhamis, yayin wani taron tattaunawa da jama’a da aka shirya gudanarwa a yankin Oregun da ke Jihar Legas.
Maharan, wadanda ke dauke da makamai irin su adduna, sanduna da duwatsu, sun kutsa cikin wurin da ake gudanar da taron, suka tarwatsa shi tare da haddasa firgici a tsakanin mahalarta.

Kara karanta wannan
Kwana 2 kafin ziyarar Tinubu, 'yan bindiga sun kewaye gari sun buɗe wa mutane wuta

Source: Twitter
The Cable ta ruwaito cewa lamarin ya tilasta wa mutanen da suka halarci taron watsewa ta hanyoyi daban-daban domin tsira da rayukansu, yayin da maharan suka ci gaba da tayar da hargitsi a wurin.
Yadda Obi ya lashe Legas a 2023
Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na NDC, ya lashe zaben shugaban kasa na 2023 a Jihar Legas, wadda ake yi wa kallon daya daga cikin manyan tushen jam’iyyar APC.
Mataimakinsa a zaben shekarar 2027 shi ne Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan Jihar Kano.
Hadin gwiwar ‘yan siyasar biyu na daga cikin abubuwan da suka jawo hankalin magoya bayan jam’iyyar a yayin shirye-shiryen zaben mai zuwa.
Yan daba sun tarwatsa taron NDC
Kafin barkewar hargitsi a wurin taron, komai na tafiya cikin kwanciyar hankali. An ga magoya bayan Obi da Kwankwaso suna rawa da rera wakoki cikin farin ciki, yayin da suke jiran fara taron tattaunawar.
Mahalarta taron sun taru ne domin shiga tattaunawar da aka shirya gudanarwa, amma yanayin ya sauya kwatsam bayan wasu ’yan daba suka mamaye wurin.
Da misalin karfe 11:00 na safe ne maharan suka isa wurin, inda suka fara kokarin kai wa magoya bayan NDC hari.
Masu dauke da makaman sun yi amfani da adduna, sanduna da duwatsu wajen tayar da hankali tare da tarwatsa taron.
Mutane sun tarwatse a wurin taron
Rahoton ya nuna cewa tun kafin su kutsa cikin babban zauren taron, ’yan dabar sun yi yunkurin shiga wurin, amma magoya bayan NDC suka yi turjiya tare da hana su shiga da farko.

Source: Facebook
Sai dai daga bisani maharan suka ci gaba da kokarinsu na kutsawa cikin zauren, lamarin da ya jawo barkewar hargitsi da tarwatsa mutane a wurin taron.
Harin na Oregun ya faru ne yayin da magoya bayan jam’iyyar NDC ke gudanar da taron tattaunawa da jama’a, wanda aka shirya domin haduwa da masu ruwa da tsaki da kuma masu goyon bayan Obi da Kwankwaso.
Kun ji cewa
Asali: Legit.ng
