Ministocin Tinubu 9 da ake sa Ran za Su Fito Takarar Gwamna a 2027

Ministocin Tinubu 9 da ake sa Ran za Su Fito Takarar Gwamna a 2027

  • Wasu ministocin gwamnatin Bola Tinubu na nuna alamun shirin komawa filin fafatawa a zaben gwamna a jihohinsu a 2027
  • Ministocin na cikin wadanda suka tsaya takara a 2023 ko kuma suka bayyana sha'awarsu a baya, kuma yanzu suke kokarin gina karfinsu a siyasance
  • Wasu daga cikin ministocin sun fara nuna sha’awar sake komawa takara, musamman a jihohin Zamfara, Osun, Oyo da Bauchi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Bayan shafe shekara guda a gwamnatin Bola Tinubu, wasu daga cikin ministoci sun fara bayyana burinsu na sake komawa takarar kujerun gwamna a shekarar 2027.

Wannan yunkuri na zuwa ne yayin da wasu daga cikinsu suka kasance 'yan takara a zaben 2023, yayin da wasu kuma suka bayyana sha'awarsu a baya amma ba su samu damar tsayawa ba.

Bello Matawalle
Ministocin da ake sa ran za su fito takarar gwamna a 2027. Hoto: Bello Matawalle|Mohammed Idris Malagi|Yusuf Maitama Tuggar
Asali: Facebook

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa nadin da aka musu na ministoci wata hanya ce ta karfafa su don su ci gaba da kasancewa da tasiri da kuma samun damar sake tsayawa takara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2027: Ministocin da ake ganin za su yi takara

Daga cikin ministocin da ake ganin za su nuna sha’awa akwai ministan yada labarai, Ahmed Idris Malagi wanda ya tsaya takara a jihar Neja a 2023 amma bai samu tikitin jam’iyyar APC ba.

Sauran sun hada da ministan jin kai da rage talauci, Nentawe Yiltwada Goshwe da minista Adegboyega Oyetola.

Ana ganin karamin ministan harkokin tsaro, Bello Matawalle da ministan makamashi, Adebayo Adelabu wadanda suka tsaya takara a 2023 za su iya kara neman matsayin da suka baro.

Saidu
Ana hasashen ministan sufuri zai nemi takarar gwamna a Gombe a 2027. Hoto: Saidu Ahmed Alkali
Asali: Facebook

Haka kuma, akwai Sanata Abubakar Kyari da Yusuf Tuggar wadanda suka nuna sha'awar takarar gwamna a jihohin Borno da Bauchi a baya.

Yadda siyasar 2027 za ta iya kasancewa a jihohi

A wasu jihohi kamar Zamfara da Osun, Matawalle da Oyetola za su iya sake fafatawa da abokan hamayyarsu na baya bayan shan kaye da suka yi a 2022 da 2023.

A jihar Oyo, Adelabu na iya cin moriyar kammala wa'adin gwamna Seyi Makinde da kuma kasancewar Tinubu a matsayin shugaban kasa daga yankin Yammacin Najeriya.

A Gombe, akwai alamun cewa Saidu Alkali zai iya fitowa takara kasancewar Inuwa Yahaya zai kammala wa'adi na biyu.

A Bauchi kuwa akwai alamar za a iya fafatawa tsakanin ministan lafiya, Muhammad Ali Pate da ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar wajen neman tikitin APC.

Ga jerin ministocin da ake ganin na da niyyar tsayawa takarar gwamna a zaben 2027 a jihohinsu:

1. Ahmed Idris Malagi – Ministan Harkokin Yada Labarai

  • Ya tsaya takarar gwamna a jam’iyyar APC a Jihar Neja a 2023 amma bai samu nasara ba.

2. Nentawe Yiltwada Goshwe – Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci

  • Ya tsaya takarar gwamnan Plateau a ƙarƙashin APC a 2023.

3. Adegboyega Oyetola – Ministan Harkokin Teku

  • Tsohon gwamnan Osun, ya fadi a yunkurinsa na neman wa’adi na biyu a 2022.

4. Bello Matawalle – Karamin Ministan Tsaro

  • Tsohon gwamnan Zamfara, ya sha kaye a zaɓen 2023.

5. Adebayo Adelabu – Ministan Makamashi

Ya tsaya takarar gwamna a Oyo a ƙarƙashin jam'iyyar Accrod a 2023.

6. Sanata Abubakar Kyari – Ministan Noma

  • Tsohon shugaban APC na Jihar Borno, ya nuna sha’awar gwamna a baya.

7. Yusuf Maitama Tuggar – Ministan Harkokin Waje

  • Ya taba bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar gwamnan Bauchi.

8. Sanata Saidu Ahmed Alkali – Ministan Sufuri

  • Ana hasashen zai nemi gwamnan Gombe a 2027.

9. Muhammad Ali Pate – Ministan Lafiya

  • Ana hasashen zai nemi gwamna a Bauchi

Yahaya Bello ya ce ba zai yi takara a 2027 ba

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ba zai yi takara a shekarar 2027 ba.

Yahaya Bello ya bayyana haka ne yayin da aka fara maganar cewa zai buga takara da Bola Tinubu a zabe mai zuwa.

Tsohon gwamnan da yake da matsala da hukumar EFCC ya bayyana cewa yana goyon bayan Bola Tinubu dari bisa dari a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng