Kungiyar CAN Ta Dawo da Batun Zainab da Aka Ce Ta Bar Musulunci a Jihar Zamfara
- Kungiyar CAN ta yabawa gwamnatin Zamfara bisa yadda ta fito ta yi bayani kan batun Zainab da ake zargin ta sauya addini
- A wata sanarwa da CAN ta fitar, ta ce bayanin da gwamnatin ta yi ya rage zafin lamarin amma duk da haka za ta yi bincike
- CAN ta ce za ta ci gaba da ƙoƙarin kare ƴancin kowane ɗan Najeriya na yin addinin duk da ya ga dama ba tare da fuskantar tsangwama ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), reshen jihohin Arewa 19 da Abuja, ta tsoma baki kan batun Zainab Muhammad, wacce aka yaɗa jita-jitar ta canza addini.
CAN ta bayyana jin daɗinta bisa yadda gwamnatin jihar Zamfara ta fito ta yi bayani dalla-dalla tare da ƙaryata raɗe-raɗin da ake yaɗawa.

Asali: Twitter
Tun farko, Sahara Reporters ta wallafa rahoton cewa budurwar mai suna, Zainab na fuskantar shari'a a jihar Zamfara saboda ta bar addinin musulunci zuwa kiristanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya kuma yi ikirarin cewa akwai yiwuwar kotun shari'ar musulunci ta yanke mata hukuncin kisa, lamarin da ya tayar da ƙura a kafafen sada zumunta.
Zainab: CAN ta yabawa gwamnatin Zamfara
Jim kaɗan bayan haka, gwamnatin Zamfara ta fito ta karyata rahoton, ta ce matar da ake yaɗa hotonta ba ƴar Najeriya ba ce kuma babu wata shari'a kan sauya addini a jihar.
Da take martani kan lamarin, CAN ta yabawa gwamnatin Zamfara bisa yadda ta ba da hujjar da ke tabbatar da babu wata shari'a makamanciyar haka da ake yi a Zamfara.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban CAN na Arewa, Rev. Dr. Joseph John Hayab da sakatare, Bishop Mohammed Naga, suka sanyawa hannu a ranar Alhamis, rahoton Leadership.
CAN ta sha alwashin kare haƙƙin addini
CAN ta ce duk da bayanan gwamnatin Zamfara ya rage ƙuncin lamarin, ya zama dole a ci gaba da sa idanu, domin idan aka gano wani abu daga baya, za a iya samun matsala.
“Muna tabbatar wa Kiristoci a Arewa da ma faɗin Najeriya cewa CAN ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen binciko gaskiya da kawo ƙarshen kowane irin tsangwama ko gallazawa da ya shafi addini.”

Asali: Original
CAN ta yaba da kokarin ’yan sanda, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da ƙungiyoyin matasa da suka taimaka wajen dakile yiwuwar tashin hankali.
Ta kuma ja hankalin Kiristoci da su zauna lafiya, su ci gaba da bin doka da oda, tare da yin addu’a, yayin da ƙungiyar ke kokarin kare ’yancin kowanne ɗan Najeriya ya yi addinin da yake so ba tare da tsoro ko barazana ba.
Abin da gwamnatin Zamfara ta ce kan Zainab
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Jihar Zamfara ta karyata rahoton da ke cewa wata mace mai suna Zainab na fuskantar shari'a kan canza addini.
Ta ce raɗe-raɗin ya taso ne daga shafukan sada sumunta kuma wasu masu neman jan hankali ne kawai suka ƙirƙire shi amma ba gaskiya ba ne.
Gwamnatin Zamfara ta bayyana cewa hoton da ake yaɗawa na matar da ta koma kiristanci ba ƴar Najeriya ba ce, sunanta Aalia, kuma ƴar Texas ce a kasar Amurka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng