Iran ta Kaddamar da Farmaki kan Sojojin Amurka, Ta Fitar da Gargadi ga Trump
- Rahoto ya nuna cewa kasar Iran ta ce dakarunta sun kai hari kan wani muhimmin na’urar sadarwar sojojin Amurka da ke Bahrain
- Harin na zuwa ne a matsayin martani kan abin da Iran ta bayyana a matsayin harin sama da aka kai kan hasumiyar sadarwa ƙasar ta
- Dakarun IRGC sun yi gargaɗin cewa a shirye suke su ci gaba da kai hare-hare idan Amurka da ƙawayenta suka sake kai mata farmaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Bahrain – Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun bayyana cewa sun kai hari kan wani sansanin na’urar sadarwa da Amurka ke amfani da shi wajen gano barazanar hare-hare a ƙasar Bahrain.
Iran ta ce harin martani ne kan abin da ta bayyana a matsayin harin sama da aka kai kan hasumiyar sadarwa a kudancin ƙasar.

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta rahoto cewa sanarwar ta fito ne sa'o'i bayan da kamfanin dillancin labaran ƙasar Iran (IRNA) ya ruwaito cewa an kai hari kan birnin tashar jiragen ruwa na Sirik da ke lardin Hormozgan ranar Alhamis.
Iran ta yi barazanar kai hare-hare
A cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya wallafa, IRGC ta bayyana harin a matsayin gargaɗi mai ƙarfi ga abokan gabanta da ta zarga da kai mata hare-hare.
Dakarun sun ce matakin ya biyo bayan jerin hare-haren sama da kuma safarar man fetur da suka ce ana yi a mashigar ruwan Hormuz.
A cikin sanarwar, IRGC ta ce:
“Idan aka sake samun waɗannan take-take da ayyukan cin zarafi, rundunar sama ta IRGC a shirye take ta tunkare su ba tare da wani iyaka ba.”
Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, babu wata sanarwa kai tsaye daga gwamnatin Amurka ko Bahrain kan ikirarin harin.
Amurka na da soji a Bahrain
Bahrain na da hedikwatar rundunar sojojin ruwan Amurka ta Fifth Fleet, wadda ke da alhakin ayyukan sojin ruwan Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.
Rahoton ya nuna cewa wannan shi ne karon farko tun farkon watan Satumban 2026 da Iran ta yi ikirarin kai hari kan kadarorin sojin Amurka a wata ƙasa da ke yankin Gulf.
Harin na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar tsaron Isra’ila ta umarci sojojinta da ƙara shirin tunkarar yiwuwar kai hari kan Iran, kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.

Source: Facebook
Haka kuma, babban jami’in tsaron Iran, Mohsen Rezaei, ya yi gargaɗin cewa idan Amurka ta sake fara yaƙi da ƙasarsa, duk wani sansanin soji da zai taimaka mata, daga yammacin Asiya har zuwa Turai, zai zama halastaccen wurin da Iran za ta kai hari.
A nasa ɓangaren, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce a shirye yake ya sake komawa yaƙi idan ƙoƙarin diflomasiyyar da Qatar ke jagoranta ya gaza samar da yarjejeniya.
Iran ta nuna rumbun makamai
A wani labarin, kun ji cewa sabon wurin ajiyar makamai masu linzami da dakarun kare juyin juya halin Musulunci suka bayyana ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’ummar ƙasar.
Rahotanni sun nuna cewa kafafen yaɗa labaran Iran sun wallafa hotunan Ali Abdollahi, babban hafsan hafsoshin sojojin ƙasar, da Majid Mousavi a wajen.
Sai dai ba a bayyana inda wurin yake ba ko kuma ranar da jami’an suka kai ziyara. Wasu ’yan ƙasar sun nuna fushinsu kan yadda gwamnati ke kashe kuɗi wajen ƙara ƙarfin makamai.
Asali: Legit.ng


