Kwara: Mutane 2 Suna Kwance a Asibiti cikin Wani Hali bayan Hatsarin Jirgin Sama
- Wani jirgin horas da dalibai na Diamond ya fadi a Ilorin yayin gwajin sauka bisa na'ura, mutane biyu sun jikkata
- Hukumar NSIB ta tabbatar da faruwar hatsarin a hanyar sauka na filin jirgin Ilorin, ta ce jirgin ya kauce daga hanya ya tsaya a ciyawa
- Shugaban NSIB, Alex Badeh, ya ce za su binciki lamarin sosai domin gano musabbabin hatsarin, ya bukaci mutane su guji yada jita-jita
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara - An tabbatar da samun raunuka bayan wani jirgin sama ya samu matsala a jihar Kwara.
An ce mutane biyu sun jikkata bayan wani jirgin Diamond na makarantar horar da masu tuka jirgi a Ilorin ya fadi.

Asali: Original
Hatsarin jirgin sama ya raunata mutum 2
Ma'aikatar jirgin saman ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:00 na yamma, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hatsarin jirgin ya faru ne yayin da ake gwajin sauka bisa na’ura a kan hanyar filin jirgin sama na kasa da kasa a Ilorin.
Gwajin sauka da na’ura na nufin tuki da kayan na’ura kawai ba tare da duba waje ba, sai ta hanyar gilashi mai hana gani.
Babu wanda ya mutu a hatsarin, amma an garzaya da mutum biyu da ke cikin jirgin asibiti, Sahara Reporters ta tabbatar da rahoton.
Menene ya jawo hadarin jirgin saman?
A gefe guda, Hukumar Binciken Hadurra ta Kasa (NSIB) ta ce ta fara bincike domin gano musabbabin faduwar jirgin.
Hukumar ta ce hatsarin ya faru ne lokacin da jirgin ke kokarin sauka bisa na’ura a kan hanyar jirgi kuma ya tsaya a gefen ciyawa.
NSIB ta ce:
“Mutane biyu ne a cikin jirgin. Duk sun jikkata sosai, kuma an dauke su da gaggawa zuwa asibiti.”
“Za mu tabbatar da tsaron wurin, tara shaidu, yin hira da masu gani da ido, da duba bayanai don gano dalilin hatsarin.”
- Cewar hukumar

Asali: Twitter
Matakin da hukumar NSIB ke shirin ɗauka
Hukumar NSIB ta bayyana cewa tawagarta daga Abuja na shirin zuwa Ilorin domin bincike kai tsaye a wurin da hatsarin ya faru.
Shugaban NSIB, Kyaftin Alex Badeh, ya ce:
“Zuciyarmu na tare da wadanda suka jikkata, kuma muna godiya da yadda aka dauki mataki cikin gaggawa.
"Yanzu dai abin da yafi muhimmanci shi ne gano ainihin abin da ya janyo hatsarin. Bincike irin wannan na kara inganta tsaro.”
- Cewar Badeh
Hukumar ta bukaci jama’a da kafofin yada labarai su guji yada jita-jita, su jira bayani daga hukumomi.
An hana jirgin Sanatoci sauka a Taraba
Kun ji cewa Sanata David Jimkuta ya nuna ɓacin ransa kan yadda aka hana saukar sanatoci 18 da ya gayyato zuwa wurin taron rabon kayan tallafi.
Jimkuta ya ce makircin siyasa aka sanya wajen hana jirgin da ya ɗauko sanatocin sauka a filin jiragen sama na Kashimbila a jihar Taraba.
Sanatan ya ce matsalar ba za ta hana shi aiwatar da abubuwan alherin da ya yi niyya ba, yana mai cewa mutane da yawa sun koma gida da farin ciki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng