Trump da Netanyahu sun yi kaca kaca a waya saboda lamarin yakin kasar Iran

Trump da Netanyahu sun yi kaca kaca a waya saboda lamarin yakin kasar Iran

  • Rahotanni sun ce Shugaban Amurka Donald Trump da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu sun yi cacar baki mai zafin gaske
  • Israila tana so a sake kai hare-hare kan Iran amma shi Shugaban Amurka na kokarin ganin an cimma matsaya ne ta hanyar diflomasiyya
  • Ana zargin cewa wannan sabani game da yaki a kasar Iran ya jawo zazzafar muhawara tsakanin Trump da Netanyahu ta wayar salula

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

America - Donald Trump na kasar Amurka da Firayim Ministan Israila, Benjamin Netanyahu sun yi kaca-kaca a wata wayar salula.

An samu sabani tsakanin shugabannin duniyan da suka yi magana ta wayar tarho dangane da batun cigaba da yaki da Jamhuriyyar Iran.

Gidan talabijin Fox ya rahoto cewa shugaban na Amurka ya yi magana da takwaransa na Israila kan maganar dawo da yakin Iran.

An ce Benjamin Netanyahu yana so komai ya dawo danye, a cigaba da yi wa Jamhuriyyar Musulunci ta kasar Iran luguden makamai.

Kara karanta wannan

Na gaban goshin Tinubu ya fadi wa suke shakka a 2027, banda Atiku da Obi

Shi kuma Donald Trump ya zabi a bi hanyar lalama domin ganin an shawo kan rikicin da ake yi.

Jami'in Israila ya karyata labarin

Wata majiya ta ce wayar da shugabannin biyu suka yi ta dauki zafi, sai dai ofishin Firayim Ministan Israila ya ce haka abin ya kasance ba.

Majiya daga Israila sun nuna cewa ba a kai ga yin sa-in-sa lokacin da shugabannin suka yi waya ba.

Sai dai ba wannan ne karon farko da aka ji sabani ya shiga tsakanin Trump da shi Netanyahu wanda yake fuskantar barazana a Israila ba.

Idan labarin ya tabata, an ce sai da ta kai ana cacar baki a wayar da aka yi a karshen makon jiya, sai dai babu tabbacin wannan magana.

Wani jami’in Israila ya tabbatar da cewa shugabanni sun yi waya amma abin bai wani yi zafi ba.

Abin da majiyar gwamnatin Amurka ta shaida

Manyan jami’an gwamnatin Amurka suna ganin har gobe su ne ke da iko da mashigar Hormuz kuma tattalin arzikin Iran yana rugujewa a yanzu.

Kara karanta wannan

Yusuf Datti da sauran ‘yan a mutun Peter Obi 10 da suka watsar da tafiyar shi

Wani babba a Washington ya shaida cewa wuka da nama suna hannun Trump kuma sun yi Imani zai dauki matakin da duk ya dace da Amurka.

Israila tana so a hambarar da daular Iran

Ita ma jaridar Financial Times ta ce Netanyahu yana ta kiran Trump a duk ranar duniya saboda ganin ya zuga shi an cigaba da yakar Iran.

A halin yanzu Firayim Ministan na Israila wanda ba a taba yin wanda ya dade a mulki irin shi ba, ya rasa kujerun jam’iyarsa a zaben da aka ayi.

Shi a wurin shi, idan ana so a iya maganin Iran shi ne a hambarar da shugabannin da ke kan mulki.

Ana zargin cewa kasar Iran ta cigaba da kokarin ganin ta samu makamin nukuliya don haka ake so a kifar da Ayatollah Mojtabah Khameni.

Duk da yadda Netanyahu ya dace, an ce Trump ya fara jan jiki daga lamarin Iran, yana maida hankali kan halin da tattalin Amurka yake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng