Bayan Ya Koma APC, Tinubu Ya ba Tsohon Gwamnan Katsina, Ibrahim Shema Muƙami

Bayan Ya Koma APC, Tinubu Ya ba Tsohon Gwamnan Katsina, Ibrahim Shema Muƙami

  • Shugaba Bola Tinubu ya nada tsohon gwamnan Katsina, Ibrahim Shehu Shema a matsayi a hukumar raya birnin tarayya, FCDA
  • Shema ya gaji Shehu Hadi Ahmad kuma zai jagoranci ci gaban Abuja, musamman wajen magance cunkoso da matsalar gidaje
  • Mutane da dama sun yaba da nadin Shema da cewa zai kawo sauyi musamman wajen shawo kan matsalolin sufuri da rashin arahar gidaje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema a gwamnatinsa.

Tinubu ya nada Shema a matsayin sabon shugaban majalisar da ke sa ido a kan aikin hukumar FCDA domin bunkasa babban birnin Abuja.

Tinubu ya nada Shema muƙami a gwamnatinsa
Tinubu ya gwangwaje da Ibrahim Shema da mukami a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Tinubu ya ba Shema muƙami a gwamnati

An sanar da nadin ranar Juma’a, kuma ana sa ran zai taimaka wajen cika burin sauya Abuja zuwa birni na zamani, kamar yadda @MSIngawa ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar wata sanarwa daga fadar shugaban kasa, Tinubu ya nuna kwarin gwiwarsa kan Shema, yana cewa yana da kwarewa wajen mulki da ci gaba.

Ibrahim Shema ya shugabanci jihar Katsina daga 2007 zuwa 2015 inda ya yi fice wajen ci gaban ababen more rayuwa, ilimi da lafiya.

An kafa Hukumar FCDA ne domin lura da ci gaban ababen more rayuwa a Abuja tun shekarar 1976 kuma tana da muhimmanci wajen tsara birnin.

Sanarwar ta ce:

“Kwarewar Shema da hangen nesansa sun dace da kudirinmu na hanzarta ci gaban gine-gine da tsara Abuja bisa tsari.”

Nadin Shema ya zo a lokaci mai muhimmanci da Abuja ke fuskantar matsaloli kamar yawaitar jama'a, karancin gidaje da bukatar karin ayyuka.

Shema ya maye gurbin Injiniya Shehu Hadi Ahmad wanda ya mayar da hankali kan hanyoyi da ababen more rayuwa inda ake da ran rantsar da Shema mako mai zuwa.

Hakan nan, hadimin Shema a bangaren yada labarai, Kwamred Yusuf Lawal Mai-iyali ya tabbatar da labarin a shafinsa na Facebook.

Sababbin nade-nade da Tinubu ya yi
Tinubu ya yi sababbin nade-nade a hukumomi daban-daban. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Sauran nade-nade da Tinubu ya yi

Akwai karin hukumomi da Tinubu ya yi nade-naden shugabanni da za su jagorance su domin inganta aikin gwamnati.

1. Yazid Shehu Umar Danfulani daga Zamfara - NAIC

2. Hamza Ibrahim Baba daga Kano - GEEP

3. Abubakar Umar Jarengol daga Adamawa - NAIC

4. Sama’ila Audu daga Katsina - NSITF

5. Kwamred Isa Aremu daga Kwara - MINILS

6. Abdullahi Barkiya daga Katsina - NALDA

7. Farfesa Musa Garba Mai Tafsiri daga Kebbi - Hukumar yaƙi da jahilci

8. Farfesa Garba Hamidu Sharubutu daga Benue - Cibiyar binciken harkokin noma

9. Abdullahi Mohammed daga Katsina - Hukumar hadin kan Najeriya da São Tomé & Príncipe

10. Sanata Tijjani Yahaya Kaura daga Zamfara - Cibiyar horas da jama'a

Nadin mukamai: Gwamnatin Tinubu ta ba da hakuri

A wani labarin, Fadar shugaban kasa ta ce Bola Tinubu bai nuna wariyar addini ko kabila wajen nada mukamai tun da ya hau karagar mulki

Gwamnatin tarayya ta ce tun yana Gwamnan Lagos, ya ba kowa dama, tare da bai wa ’yan kowane yanki mukamai bisa cancanta.

A kokarin fitar da adadin mutanen da Bola Tinubu ya nada a Arewa da Kudu, gwamnatin ta yi kuskure kuma ta ba 'yan Najeriya hakuri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.