Kaduna: Yara da Magoya Bayan El Rufai Sun Yi Watsi da ADC, Sun Koma Jam’iyyar APC

Kaduna: Yara da Magoya Bayan El Rufai Sun Yi Watsi da ADC, Sun Koma Jam’iyyar APC

  • Wasu magoya bayan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, sun rabu da ADC kuma sun bi APC domin mara wa Gwamna Uba Sani baya
  • Wadanda suka sauya sheka sun zargi ADC da nuna musu wariya, rashin adalci wajen rabon tikitin takara da rashin kyakkyawan shugabanci
  • Ibrahim Khalil Dan Kasa ya koka da cewa ba su san inda Isa Ashiru Kudan ya dosa ba duk da sun yi watanni suna tallar ‘dan takaran na ADC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kaduna - Daruruwan magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai sun fice daga ADC zuwa jam’iyyar APC, yanzu suna tare da Uba Sani.

‘Yan kungiyoyin El-Rufai Boys Vanguard, Nasiriyya Youth, tsofaffin masu neman takara a ADC da wasu shugabannin jam’iyyar a Kaduna sun sauya-sheka.

Masoyan Nasir El-Rufai sun sanar da barin ADC

Mutanen da suka sauya sheka sun sanar da ficewarsu daga ADC ne a ranar Alhamis, lokacin da suka gudanar da taron manema labarai a cewar jaridar Punch.

Kara karanta wannan

An yi arangama da 'yan daba suka kai hari wurin taron magoya bayan Obi da Kwankwaso

An yi wannan taro ne a sakatariyar kungiyar ’yan jarida ta Najeriya (NUJ) da ke garin Kaduna. A nan aka ji cewa sun janye goyon bayansu ga Hon. Isa Ashiru Kudan.

Kungiyar da ta yi amfani da sunan Coalition of El-Rufai Youth Groups ta rika rera taken nuna goyon baya, suna cewa “Ba mu yi” da kuma “ADC ta mutu a Kaduna”

A kuma ji wasu suna ta cewa “Uba Sani so biyu ne”, yayin da suke bayyana goyon bayansu ga gwamnan.

Da yake karanta sanarwar kungiyar, Ibrahim Khalil Dan Kasa ya ce sun yanke shawarar sauya sheka ne bayan tattaunawar da suka yi a dukkan shiyyoyin jihar.

Ibrahim Khalil Dan Kasa ya nemi tsayawa takarar Majalisar dokokin jihar a mazabar Unguwan Sanusi karkashin ADC amma bai samu tikiti a 2027 ba.

Tsohon gwamna El-Rufai ya rasa mutanensa

Dan Kasa ya yi ikirarin cewa sauya shekar ta kunshi sama da masu kula da rumfunan zabe 2,000, tsofaffin ’yan takara da kuma wasu masu neman takara.

Masu wayar da kan matasa da shugabannin jam’iyya daga sassan Kaduna sun bi wannan jirgi.

Kara karanta wannan

Kwana 2 kafin ziyarar Tinubu, 'yan bindiga sun kewaye gari sun buɗe wa mutane wuta

Vanguard ta rahoto cewa ya danganta matakin nasu da rikice-rikicen cikin gida, nuna wariya ga wasu mambobi da hana wadanda suke so samun damar takara.

Abin bai tsaya a nan ba, ya zargi jam’iyyar ADC da rashin kyakkyawar manufa ta siyasa a jihar.

Masu sauya shekar sun zargi shugabannin kungiyar El-Rufai Youth Movement da gaza kare ‘ya ‘yanta daga cin zarafi da kuma nuna musu halin ko-in-kula.

A cewar Dan Kasa, rashin jin dadinsu ya kara tsananta ne bayan tsarin zaben ’yan takarar ADC.

Tsofaffin yaran na El-Rufai suna ganin an yi watsi da mutanensa da ya ba su shawarar su tsaya takara a mazabun Kawo da Doka Gabasawa a Majalisar jiha.

Dalilin watsi da 'dan takaran gwamnan ADC

Ya kara da cewa duk da sun shafe watanni bakwai suna tallar Isa Ashiru da ADC, har yanzu ba su ga cikakken tsarin manufofi ko shirin sa g jihar Kaduna ba.

Dan Kasa ya kuma zargi wasu ‘yan tawagar yakin neman zaben Ashiru da sukar gwamnatin El-Rufai don haka suka yanke shawarar bin gwamna Uba Sani.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban majalisa ya ga ta kansa da ya yi ƙokarin tallata Tinubu a taron jama'a

Sun ce Uba ya nuna jajircewa wajen ci gaba da ayyukan raya kasa, bunkasa abubuwan more rayuwa, kawo sauyi a yankunan karkara da adalci a gwamnati.

Ya jinjina wa gwamna bisa kammala sama da 80% na muhimman ayyukan gine-gine da raya ababen more rayuwa a birane, wadanda gwamnatin baya ta fara.

Kungiyar ta kuma yaba wa kokarin gwamnan mai-ci wajen karfafa zaman lafiya tsakanin mabiya addinai da kabilu daban-daban da kuma ba matasa dama.

Takarar Atiku Abubakar a ADC tana tangal-tangal

Idan INEC ta karbi sabon umarnin kotu da ya soke shugabancin David Mark, an ji labari ba abin mamaki ba ne a yi waje da 'yan takaran ADC a 2027.

Za a yi zama a mako mai zuwa domin yanke matsaya kan rikicin shugabancin ADC bayan kotun Tarayya ta soke shugabancin David Mark da mutanensa.

Hukumar ta bakin wani kwamishinanta, ta ce za ta jira samun cikakken takardar hukuncin kotu kafin ɗaukar mataki kan tikitin Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng