Bidiyon Sanusi II da Mataimakin Gwamna yayin Addu'ar Cika Shekara 1 a Sarautar Kano

Bidiyon Sanusi II da Mataimakin Gwamna yayin Addu'ar Cika Shekara 1 a Sarautar Kano

  • Sarkin Kano, Sarki Muhammadu Sanusi II, ya karbi bakuncin mataimakin gwamna domin zaman addu'o'i na musamman a babban masallacin Gidan Rumfa
  • An shirya zaman ne domin nuna godiya ga Allah bayan cikarsa shekara daya da komawarsa kujerar sarautar Kano bayan sauke shi da aka yi
  • Sanarwa daga shafin Sanusi II Dynasty ta bayyana cewa an gudanar da zaman tare da halartar Kwamred Aminu Abdulsalam Gwarzo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Sarkin Kano ya shirya gudanar da addu'o'i na musamman bayan sake dawowa kujerar sarauta.

Basaraken ya karbi bakuncin mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamred Aminu Abdulsalam Gwarzo.

Sarki Sanusi II ya yi addu'o'i na musamman a Kano
Sarki Sanusi II ya gudanar da addu'o'i bayan cika shekara 1 a sarauta. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin Sanusi II Dynasty ya wallafa a shafin Facebook a yau Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Musabbabin rigimar sarauta da ake yi a Kano

A ranar Alhamis 23 ga watan Mayun 2024, Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya dawo da Muhammadu Sanusi II kan karagar sarauta bayan shafe shekaru a kasa.

Tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ne ya tsige Sarki Sanusi a shekarar 2020 bayan kirkirar wasu masarautu a Kano.

Aminu Ado ya kalubalanci matakin Abba Kabir

Tun bayan dawo da shi kan karaga, aka fara takun-saka da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero wanda har ya kai ga kotu.

Aminu Ado ya kalubalanci cire shi a kan sarauta da kuma rusa masarautun da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkira wanda ya kawo shi mulki.

Tun daga wancan lokaci ake ci gaba da fafatawa a kotu yayin da kotuna da dama suka yi hukunce-hukunce mabambanta.

A halin yanzu, kowane ɓangare da ke rigima kan sarautar na jiran hukuncin kotun koli wanda ake tunanin zai raba gardama kan matsalar.

Sanusi II ya yi godiya bayan dawo wa sarauta
An gudanar da addu'o'in cikar Sanusi II shekara 1 a sarautar Kano. Hoto: @masarautarkano.
Asali: Twitter

Bidiyon Sanusi II da mataimakin gwamnan Kano

An wallafa bidiyon wanda Sarkin ke tarbar Kwamred Aminu Abdulsalam Gwarzo domin halartar taron addu'o'i na musamman wanda aka gudanar a babban masallacin Juma'a.

An shirya hakan ne domin godiya ga Allah bayan Sanusi II ya cika shekara daya da dawowa sarautar Kano wanda ke cike da matsaloli tun farko.

A cikin sanarwar, shafin ya yi rubutu kamar haka:

"Fitowar Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Dr. Khalifa Muhammad Sanusi II, CON yayin da ya karbi bakuncin mataimakin gwamnan Kano, Kwamred Aminu Abdussalam domin gabatar da zaman addu’a ta cika shekara daya da dawowar Sarki karagar mulkin Kano.
"An gudanar da zaman a babban masallacin Juma’a na birnin Kano da ke Gidan Rumfa."

Sarki Sanusi II ya naɗa sabon Turakin Kano

Mun ba ku labarin cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya nada sabon Turakin Kano bayan nada Galadima domin maye gurbin marigayi.

Sarkin ya nada Mahmud Ado Bayero a matsayin Turakin Kano bayan sauye-sauye a masarautar da aka samu tun bayan hawa sarauta da Sanusi II ya yi.

Hakan na zuwa ne duk da rikicin masarautu bai kare ba a Kano, dukan sarakuna biyu sun ci gaba da nade-naden sarauta a fadar jihar

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.