ICPC Ta Kwato Sama da Naira Biliyan 5 daga Wasu Kananan Hukumomi a Jihohi 7 da Abuja
- Hukumar ICPC ta ce ta kwato sama da Naira biliyan 5.3 daga asusun kananan hukumomi a jihohi bakwai da Babban Birnin Tarayya, Abuja
- Hukumar na haɗin gwiwa da NITDA domin tabbatar da cewa dukkan kananan hukumomi 774 sun riƙa wallafa bayanan kuɗaɗensu a intanet
- Shugaban ICPC ya ce sabon shirin zai taimaka wajen ƙarfafa gaskiya da riƙon amana tare da hana almundahana a matakin ƙananan hukumomi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuffuka Masu Alaƙa da Hakan (ICPC) ta waiwayi kudaden da ake turawa kananan hukumomi daga tarayya.
ICPC ta ce ta kwato sama da Naira biliyan 5.3 daga asusun kananan hukumomi a jihohi bakwai da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja, bayan gudanar da bincike kan harkokin kuɗaɗensu.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta rahoto cewa hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da kakakin hukumar ICPC, John Odey, ya fitar a ranar Alhamis, 12 ga watan Nuwamba, 2026.
Hukumar ta kuma bayyana cewa tana aiki tare da Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA) domin tabbatar da cewa dukkan kananan hukumomi 774 na wallafa bayanan kuɗaɗensu da sauran muhimman bayanai a shafukan intanet.
ICPC ta kwato kudin kananan hukumomi
Sanarwar ta ce shugaban hukumar ICPC, Dakta Musa Aliyu, ne ya bayyana hakan a jihar Nasarawa yayin ƙaddamar da shirin gwaji na samar da shafukan intanet ga ƙananan hukumomi, wanda ICPC da NITDA suka haɗa kai wajen aiwatarwa.
Aliyu ya ........ce shirin, wanda aka fara a Nasarawa, an tsara shi ne domin ƙarfafa gaskiya, riƙon amana da kuma bayyana yadda ake amfani da kuɗaɗen gwamnati a matakin ƙananan hukumomi ta hanyar amfani da fasahar zamani.
Ya bayyana cewa kuɗaɗe sama da N5.3bn da hukumar ta kwato sun nuna irin haɗarin da ke tattare da yadda ake tafiyar da kuɗaɗen jama'a a matakin ƙananan hukumomi, da kuma muhimmancin sa ido wajen hana cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan
Shugaban INEC ya tafi ƙasar waje, ya faɗa wa duniya matakin da za su ɗauka kan takarar Atiku a 2027
“ICPC ta kwato sama da Naira biliyan 5.3 bayan nazarin asusun ƙananan hukumomi a jihohi bakwai da Babban Birnin Tarayya, kuma yanzu tana ɗaukar matakin tabbatar da cewa ƙananan hukumomi suna wallafa bayanan kuɗaɗensu a intanet," in ji shi.
Hadin kan ICPC Dmda NITDA
Ya bayyana cewa NITDA za ta samar da kayan aikin fasaha da ake buƙata, ciki har da rajistar sunayen shafukan intanet, ƙirƙirar shafukan da kuma ɗaukar nauyin adana su na tsawon aƙalla shekara guda.
A nata ɓangaren, ICPC za ta samar da ƙa’idojin bayanan da za a wallafa da kuma tsarin da zai tabbatar da riƙon amana.
Aliyu ya buƙaci shugabannin ƙananan hukumomi su naɗa jami’ai na musamman da za su kula da shafukan intanet ɗin, tare da tabbatar da cewa bayanan da ake wallafawa sahihai ne kuma ana sabunta su akai-akai.
Yadda ake raba albarkatun Najeriya
Kun ji cewa ministan kuɗi, Taiwo Oyedele, ya ce jihohi da ƙananan hukumomi suna samun kusan kashi 85 cikin 100 na albarkatun Najeriya.
Ya ce gwamnatin tarayya ce matakin gwamnati mafi ƙarancin albarkatu idan aka kwatanta da nauyin ayyukan da take gudanarwa, ciki har da tsaro, tsaron cikin gida, harkokin ƙasashen waje da gudanar da zaɓe.
Asali: Legit.ng
