ADC Ta Ce Tabbas Atiku zai Shiga Takarar Shugaban Kasa na 2027
- Jam’iyyar adawa ta ADC ta tabbatar da cewa za ta shiga zaɓen 2027 duk da rikicin shugabanci da ƙalubalen shari’a da take fuskanta
- Kakakin jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, zai kasance cikin ’yan takarar 2027
- Ya zargi APCda amfani da rikicin shari’a wajen raunana jam’iyyun adawa domin Shugaba Bola Tinubu ya fuskanci ƙarancin hamayya a zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCt, Abuja – Jam’iyyar African ADC ta ce za ta shiga babban zaɓen 2027 duk da rikicin shugabanci da kuma ƙalubalen shari’a da take fuskanta.
Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, zai kasance cikin ’yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen mai zuwa.

Source: Twitter
Arise News ta rahoto cewa Abdullahi ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin wata hira da gidan talabijin ɗin, inda ya yi watsi da zargin cewa rikicin cikin gida zai hana jam’iyyar shiga zaɓen.
Ya ce:
“Zan iya tabbatar muku cewa za a gudanar da zaɓe a Najeriya a 2027, ADC za ta shiga zaɓen, kuma Atiku zai kasance a cikin takardar zaɓen.”
ADC ta zargi APC da makarkashiya
Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa rikicin shari’ar da jam’iyyar ke fuskanta ya samo asali ne daga siyasa, yana zargin jam’iyyar APC mai mulki da ƙoƙarin raunana jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027.
Ya ce tun bayan kafa ADC a matsayin haɗakar jam’iyyun adawa a shekarar 2025, sun fi ɓata lokaci a kotuna fiye da gudanar da kamfe ko gina tsarin jam’iyyar.
A cewarsa, manufar APC ita ce ta hana jam’iyyun adawa samun damar ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Abdullahi ya ce:
“Wannan ita ce manufar jam’iyyar da ke mulki. Don haka duk abin da kuke gani tun daga lokacin ba wai kawai batun adawa ba ne, abin da jam’iyyar mai mulki ke ƙoƙarin yi ne domin tabbatar da cewa ba ta fuskantar wata babbar barazana.”
Ya kuma nuna shakku kan rawar da wasu alkalai ke takawa a rikicin, yana mai cewa wasu ƙalubalen da jam’iyyar ke fuskanta sun samo asali ne daga muradun siyasa maimakon doka.
Bolaji Abdullahi ya kare ADC
Da yake magana kan hukuncin babbar kotun tarayya da ya soke kwamitin gudanarwa na ƙasa na ADC da David Mark, ke jagoranta, ya ce tsarin da suka bi wajen karɓar shugabancin jam’iyyar ya yi daidai da kundin tsarin mulkinta.
Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa ADC ta yi gyare-gyare ga kundin tsarin mulkinta, inda ta cire sharadin zama mamba na tsawon shekari biyu kafin mutum ya nemi muƙamin shugabanci a jam’iyyar.

Source: Facebook
Haka kuma, ta cire dokar da ta takaita maye gurbin jami’in jam’iyya da mutum daga yankin siyasa ɗaya da shi.
Ya ce bayan waɗannan gyare-gyare, wasu mambobin tsohon kwamitin gudanarwa na ƙasa sun ajiye muƙamansu, sannan aka rusa kwamitin a taron kwamitin zartarwa na ƙasa karo na 99 da aka gudanar a watan Yulin 2026.
Abdullahi ya ce tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Nafiu Bala, ba zai iya ikirarin ya gaji kujerar shugaban jam’iyyar ba bayan rusa kwamitin da yake cikinsa.
Nafiu Bala ya yabi Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Nafiu Bala ya bayyana cewa shi ne sahihin shugaban wani tsagin jam’iyyar bayan hukuncin kotu kan rikicin cikin gida.
Nafiu Bala ya kuma yi bayani kan yadda ya samu jami’an tsaron da ke kare shi sakamakon barazanar da ya ce yana fuskanta a Najeriya
Da yake magana kan sukar da ake yi wa Shugaba Bola Tinubu, Nafiu Bala ya ce bai dace ’yan adawa su riƙa amfani da munanan kalamai wajen jifan juna ba.
Asali: Legit.ng


