Zaben 2027: Malamin Addini Ya Hango Ministan da Zai Kawo Cikas ga Tazarcen Tinubu
- Primate Elijah Ayodele ya ce gazawar Ministan Wutar Lantarki, Tegbe Joseph, wajen magance matsalar wuta na iya shafar Tinubu a zaɓen 2027
- Malamin addinin ya koka kan yadda miliyoyin ’yan Najeriya ke shafe makonni ba tare da samun wutar lantarki ba
- Ayodele ya buƙaci Tinubu ya ɗauki mataki cikin gaggawa, yana mai cewa matsalar wuta na iya ƙara wa gwamnati fushin jama’a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja – Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya gargaɗi Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa matsalar wutar lantarki na iya kawo cikas ga ƙoƙarinsa na sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Malamin addinin ya ce idan Ministan Wutar Lantarki, Tegbe Joseph, ya gaza magance matsalar lantarkin da ke ƙara ta'azzara a Najeriya, hakan na iya shafar damar Tinubu ta samun nasara.

Source: Facebook
An bayyana wannan saƙon gargaɗi a cikin wata sanarwa mai taken, “Ministan Wutar Lantarki Zai Sa Ka Sha Kaye, ’Yan Najeriya Suna Cikin Duhu – Primate Ayodele Ya Gargaɗi Tinubu.”
Shugaban sashen yaɗa labaran malamin, Osho Oluwatosin, ne ya fitar da sanarwar ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba, 2026, sannan ya aika wa Legit.ng.
Ayodele ya koka kan matsalar wutar lantarki
Primate Ayodele ya nuna damuwarsa kan yadda miliyoyin ’yan Najeriya ke shafe makonni ba tare da samun wutar lantarki ba, yana mai cewa ma’aikatar da abin ya shafa ba ta samar da wata sahihiyar mafita ba.
“Idan wannan ministan wutar lantarki bai san abin da yake yi ba, rashin ƙwarewarsa zai yi mummunan tasiri ga damar Shugaba Tinubu.
“Duhu ya mamaye ko’ina, tsarin samar da wutar lantarki ba ya aiki, kuma wannan ya fi abin da aka gani a lokacin mulkin Adelabu muni.
“Rayukan mutane da dama na cikin haɗari saboda duhun da ’yan Najeriya ke fuskanta. Haka kuma, wannan matsala na ƙara nuna gazawar gwamnatin da ke kan mulki.”
Ya buƙaci Tinubu ya ɗauki mataki cikin gaggawa
Malamin addinin ya kuma aika saƙo kai tsaye ga Shugaba Tinubu, inda ya ce haɗa matsalar wutar lantarki da matsin tattalin arzikin da ’yan Najeriya ke fuskanta na iya sa jama’a su ƙi goyon bayan gwamnatinsa.
A cewarsa, ’yan Najeriya sun riga sun shiga mawuyacin hali sakamakon tsadar rayuwa, don haka ƙara musu wahalar rashin wutar lantarki na iya zama nauyi fiye da ƙarfinsu.
Ayodele ya ce:
“’Yan Najeriya sun riga sun fuskanci matsin tattalin arziki mai yawa, amma ga shi kuma suna fama da matsalar wutar lantarki. Wannan ya yi musu yawa, kuma idan Tinubu ya yi watsi da wannan matsala, hakan na iya jawo wa gwamnatinsa babban ƙin amincewa daga jama’a.
“Yana buƙatar ɗaukar mataki kafin lokaci ya ƙure. Waɗannan abubuwa ne na yau da kullum da gwamnati mai ɗaukar nauyin jama’a ya kamata ta samar musu. Ba wani abu ne mai yawa da ake nema ba.”
Ayodele ya bayyana waɗannan kalamai ne a matsayin gargaɗi ga Shugaba Tinubu kan yiwuwar tasirin matsalar wutar lantarki ga siyasar ƙasar gabanin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Muhammed Idris ya lissafo hanyoyin da kowane ɗan Najeriya ke amfana da mulkin Tinubu

Source: Facebook
Matawalle na son tazarcen Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa babban burinsa shi ne ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Asali: Legit.ng

