Ana Batun Hadaka, Jigo a APGA Ya ba Atiku Shawara kan Zaben 2027
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya samu shawara daga wajen jigo a jam'iyyar APGA mai alamar zakara
- Shugaban matasan APGA na ƙasa, Eze-Onyebuchi Chukwu ya buƙaci Atiku da ya haƙura da sake neman takarar shugaban ƙasa a 2027
- Jigon na APGA ya yi nuni da cewa lokaci ya yi da Wazirin Adamawa zai goyi bayan matashi domin ɗarewa kan mulkin Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban matasan jam'iyyar APGA na ƙasa, Eze-Onyebuchi Chukwu, ya ba Atiku Abubakar shawara kan zaɓen 2027.
Eze-Onyebuchi Chukuwu ya buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasan da ya haƙura da shirin sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.

Asali: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Chukwu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 23 ga watan Mayun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace shawara jigon APGA ya ba Atiku?
Jigon na jam'iyyar APGA ya nemi Atiku da ko dai ya marawa wani matashi nagari ɗan Najeriya baya, ko ya bar Shugaba Bola Tinubu ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu.
Ya ce dole ne tsofaffin ƴan siyasar Najeriya su fara miƙa ragamar jagoranci ga matasa masu hangen nesa da ƙwarewa, rahoton TheCable ya tabbatar.
“Maimaikon ya sake tsayawa takara a 2027, ya kamata Atiku ya tara abokan siyarsarsa su goyi bayan wani matashi nagari ɗan Najeriya."
“Lokaci ya yi da za a mayar da mulki hannun matasa.”
- Eze-Onyebuchi Chukwu
Chukwu ya tunatar da rawar da ya taka a matsayin mai jagorantar ƙungiyar Atikunation a Abuja a shekarar 2019, inda ya ce ya zuba lokaci da dukiya don goyon bayan Atiku, domin yana da yaƙinin cewa zai ba ci gaban matasa muhimmanci.
“Atiku ya ƙalubalanci Goodluck Jonathan a 2015, Muhammadu Buhari a 2019, da kuma Tinubu a 2023."
"Yanzu kuma yana so ya sake tsayawa a 2027, shin shi kaɗai ne ya dace da mulki? Akwai matasa nagari da dama da suka cancanta."
- Eze-Onyebuchi Chukwu

Asali: Facebook
An buƙaci a ba matasa dama
Jigon na jam’iyyar APGA ya ce dole ne a ƙi amincewa da tafiyar siyasar da ba ta bai wa matasa dama ba, yana mai cewa ƙasar nan na buƙatar juyin juya hali da zai ba sababbin jagorori damar tafiyar da shugabanci.
Chukwu ya ƙara da cewa idan Atiku ya nace sai ya tsaya takara, to zai fi kyau a goyi bayan Tinubu don ya yi wa’adi na biyu, amma sai ya bayar da tabbataccen alkawari na miƙa mulki ga matashi a 2031.
Ya ce matasan Najeriya sun shirya su marawa duk wani ɗan takara baya, matuƙar ya yi alƙawari bayyananne kuma tabbatacce na goyon bayan sauyin jagoranci a shekarar 2031.
Adebayo ba zai janyewa Atiku ba a 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban na jam'iyyar SDP, Adewole Adebayo ya ce ba zai janyewa Atiku Abubakar ba a zaɓen 2027.
Adebayo ya bayyana cewa idan suka haɗu a jam'iyya ɗaya da Atiku ba zai iya haƙura ya bar masa takara ba duk kuwa da girmama shin da yake yi.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya kuma bayyana cewa Atiku bai taɓa tuntuɓarsa kan batun haɗaka ba.
Asali: Legit.ng