An Bukaci Tinubu Ya Shiga Rikicin Hamdiyya Sharif da Gwamnatin Sokoto
- Kungiyoyin fararen hula har da Amnesty International sun rubuta ƙorafi ga Bola Tinubu kan yadda aka tsare Hamdiyyah Sharif
- Sun bukaci a saki Hamdiyyah mai shekara 17 ba tare da sharadi ba, inda suka ce ta shiga matsala ne bayan ta soki matsalar ‘yan bindiga
- Kungiyoyin sun zargi wasu jami’an gwamnati da amfani da matsayi wajen danniya da tsoratar da masu fadin gaskiya a Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyoyi fararen hula fiye da 35 sun mika ƙorafi ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu dangane da abin da suka kira danniya kan tsare matashiya ‘yar Sokoto, Hamdiyya Sharif.
A cewar ƙungiyoyin, an cafke Hamdiyya mai shekara 17 ne bayan ta yi magana kan yadda rikicin ‘yan bindiga ke kashe mutane da lalata rayuka a jiharta ta Sokoto.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kungiyoyin sun bayyana lamarin a matsayin tauye ‘yancin faɗar albarkacin baki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyoyin CISLAC, SERAP, Yiaga Africa, CDD da Amnesty sun magantu ne bayan Hamdiyya ta ɓace na wani lokaci, kafin a same ta a asibiti a Zamfara cikin yanayi da ake zargi da ƙeta ƙa’ida.
An yi zargin danne hakkin Hamdiyya
Haɗin gwiwar ƙungiyoyin ya yi zargin cewa gwamnati da wasu jami’anta na amfani da hukumomi wajen murƙushe muryoyi masu faɗar gaskiya.
The Cable ta wallafa cewa kungiyoyin sun ce hakan barazana ce ga dimokuradiyya da walwalar 'yan kasa masu fadin alabarkacin baki.
Sun yi Allah-wadai da yadda hukumomin jihar Sokoto suke ƙoƙarin hana mutane magana kan matsalolin tsaro da rashin shugabanci nagari.
Sannan sun ce tsare Hamdiyyah Sidi Sharif abu ne da ke nuna yadda ake ƙoƙarin razana matasa masu faɗar gaskiya.
Sun kuma ce babu wata hujja ta shari’a da ke tabbatar da tsare ta, suna cewa hakan wani yunkuri ne na tauye ‘yancin bil’adama da ake yawan ambata a cikin kundin tsarin mulki.
Hamdiyya: An bukaci Remi Tinubu ta yi magana
Kungiyoyin sun bukaci hukumar kare hakkin bil’adama (NHRC), da kwamitocin majalisa da ke da alhakin kare hakkin jama’a da su gaggauta bincike kan lamarin domin tabbatar da adalci.
Sun bukaci kotun Najeriya ta nuna jarumta da mutunta tsarin mulki ta hanyar tabbatar da ‘yancin fadar albarkacin baki, musamman ga matasa da mata.

Asali: UGC
Haka kuma sun roki matan shugabanni kamar Uwargidar Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu da Matar gwamnan Sokoto, Fatima Ahmed Aliyu da su tsaya tsayin daka wajen kare Hamdiyya.
An yi wa Hamdiyya allura a dajin Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa an samu bayanai kan halin da Hamdiyya Sidi Sharif ta shiga bayan sace ta a jihar Sokoto.
An samu matashiyar a wani daji, inda aka ce ta ce lafiyarta kalau a zahiri duk da tabbatar da cewa an yi mata allura a dajin yayin da ciwon kai ya kamata.
Hamdiyya ta bayyana cewa masu mutane ne sanye da kayan 'yan sanda suka tsare ta yayin da ta ke dawowa daga sayo kayan abinci a kasuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng