Tallafin 50,000: Ba a Bar Sojoji a Baya ba, Gwamna Ya Juyo kan Jami'an Tsaro

Tallafin 50,000: Ba a Bar Sojoji a Baya ba, Gwamna Ya Juyo kan Jami'an Tsaro

  • Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya sanar da tallafin N50,000 ga kowane soja da zai je ƙauyukan Maiwa da Koshebe
  • Gwamnan ya ce matakin na da nufin ƙarfafa tsaro a yankunan da Boko Haram ta kashe manoma 100 a shekarar 2020
  • Zulum ya kuma yi alƙawarin samar da kayan aiki da inganta walwalar sojojin da za su gudanar da aikin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da bayar da tallafin kuɗi na N50,000.

Gwamna Zulum ya sanar da ba da tallafin ne ga kowane soja da zai je ƙauyukan Maiwa da Koshebe domin ƙarfafa tsaro a yankunan.

Zulum zai ba sojoji tallafi
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno. Hoto: Professor Babagana Umara Zulum.
Source: Original

Zulum ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 13 ga watan Nuwamba, yayin ziyarar aiki da ya kai hedikwatar rundunar sojoji ta 24 Task Force Brigade da ke ƙaramar hukumar Dikwa, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yadda hukuncin kotu ya sake kara damuwar da Atiku da jam'iyyar ADC ke ciki

A yayin ziyarar, gwamnan ya gana da kwamandan rundunar, Birgediya Janar Aminu Gumel, inda suka tattauna hanyoyin inganta tsaro a yankunan da ke fuskantar barazanar hare-haren 'yan ta'adda.

Dalilin Zulum na ba sojoji N50,000

Gwamnan ya ce tallafin kuɗin na da nufin ƙarfafa jami'an tsaro da za su tafi ƙauyukan Koshebe da Maiwa domin kare rayukan al'umma da dukiyoyinsu.

Yankunan biyu sun sha fama da munanan hare-haren Boko Haram, musamman harin da ƙungiyar ta kai wa manoman shinkafa a Koshebe a watan Nuwamban 2020, inda ta kashe ma'aikatan gona 100.

Zulum ya jaddada muhimmancin samar da ingantaccen tsaro a yankunan domin hana sake aukuwar irin wannan mummunan lamari.

Za a tallafawa sojoji a Borno
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum. Hoto: Professor Babagana Umara Zulum.
Source: Twitter

Zulum ya magantu kan hanyar Maiduguri zuwa Ngala

Haka kuma, gwamnan ya bayyana muhimmancin tabbatar da tsaro a babbar hanyar Maiduguri–Mafa–Dikwa–Ngala.

Ya ce ziyararsa ta fi mayar da hankali ne kan gano hanyoyin ƙarfafa tsaro a wannan muhimmiyar hanyar tattalin arziki da ta haɗa Maiduguri da wasu al'ummomi a gabashin jihar Borno.

Kara karanta wannan

Barakar cikin kungiyar dattawan Arewa ta kara munana ana saura kwanaki zabe

A cewarsa, hanyar na da matuƙar muhimmanci wajen zirga-zirgar jama'a, kasuwanci da harkokin cinikayyar ƙetare.

Zulum ya ƙara da cewa tabbatar da tsaro a hanyar zai ba mazauna yankin damar yin zirga-zirga ba tare da fargaba ba, gudanar da kasuwancinsu cikin walwala da sake gina hanyoyin samun abin dogaro.

Da yake jawabi ga sojojin, gwamnan ya yi alƙawarin ci gaba da samar musu da kayan aikin gudanar da ayyukansu tare da inganta walwalarsu.

Karin bayani na tafe.....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.