Rikadawa, Mansurah da ’Yan Kannywood da Suka Bar Tafiyar Rarara da Dalilan Ficewarsu

Rikadawa, Mansurah da ’Yan Kannywood da Suka Bar Tafiyar Rarara da Dalilan Ficewarsu

Tafiyar Triple R da Dauda Kahutu Rarara ke jagoranta domin marawa Bola Tinubu baya a zaben 2027 ta fara fuskantar rikici da baraka yayin da wasu jaruman Kannywood suka fice daga kungiyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Tafiyar Bola Tinubu musamman game da zaben 2027 a Najeriya na ci gaba da samun cikas yayin da zaben ke kara fitowa.

A Arewacin Najeriya, mafi yawan masu goyon bayan Bola Tinubu na fuskantar suka duba da halin da yankin ke ciki.

Jaruman da suka bar tafiyar Rarara da Tinubu
Jarumin Kannywood, Rabiu Rikadawa, Ramadan Booth da mawaki Dauda Kahutu Rarara. Hoto: Rabiu Rikadawa, Ramadan Booth da Dauda Kahutu Rarara.
Source: Facebook

Jaruman da suka fice daga tafiyar Rarara

A masana'antar Kannywood, akwai tafiyar Triple R da mawakin siyasa a Arewa, Dauda Kahutu Rarara ke jagoranta wacce yanzu ta fara samun matsala, cewar BBC Pidgin.

Sai da an fara samun matsala saboda jaruman masana'antar da dama na ficewa daga tafiyar bayan samun baraka kan yadda ake tafiyar da ita.

Kara karanta wannan

Tinubu/Shettima: Matsayar Kiristocin Arewa kan sake daukar Kashim a mataimaki

Legit Hausa ta duba wasu dalilan jaruman Kannywood da suka fice daga tafiar bayan samun matsaloli.

1. Rabiu Rikadawa

Fitaccen jarumin Kannywood, Rabiu Rikadawa, ya sanar da ficewarsa daga ƙungiyar Triple R Kannywood for Renewed Hope.

Rikadawa ya bayyana matakin ne a ranar Juma'a, 3 ga watan Yulin 2026, yana tabbatar da cewa ya fice daga tafiyar.

Jarumin ya ce ya fice daga ƙungiyar da mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ke jagoranta, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce.

Tsohpn 'dan wasan ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne bayan rashin gamsuwa da tsarin da ake yi a cikin tafiyar.

Rikadawa ya rubuta cewa:

"Ni Rabiu Rikadawa na fita daga wannan kungiya ta 'TRIPLE "R" KANNYWOOD FOR RENEWED HOPE' a yau 3 ga watan Yulin 2026 kuma a yanzu karfe 8:30 na safe."
Ana ficewa daga tafiyar Rarara da Tinubu
Dan wasan Kannywood, Rabiu Rikadawa wanda ya fice daga tafiyar Dauda Kahutu Rarara. Hoto: Rabiu Rikadawa.
Source: Facebook

2. Yusuf Sasin

Jarumi Yusuf Sasin wanda aka fi sani da Lukman Labarina ya bayyana dalilansa na ficewa daga tafiyar Triple R, kamar yadda Daily Brief ta wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Shettima ya kai wa Tinubu ziyara bayan APC ta tabbatar da shi a tikitin 2027

Sasin ya dalilin ficewa daga kungiyar ya shafi wasu alkawura da kuma karya wasu tsare-tsare da aka shirya tun farkon fara tafiyar.

A ganinsa, ya ce idan har ana karya wasu alkawura tun yanzu, to ba za a samu abin da ake so ba a gaba saboda bin tsari shi ne komai.

Ya yi zargin cewa akwai mutum daya kacal da ya ke da iko fiye da kowa inda ya ce hakan ba karamin damuwa zai kawo ba a tafiyar.

3. Ramadan Booth

Har ila yau, matashin dan wasan Kannywood da aka fi sani da Ramadan Booth shi ma ya bayyana cewa ya fice daga tafiyar Triple R.

A ranar 3 ga watan Yulin 2026, Ramadan Booth ya bayyana a Facebook cewa ya fita daga tafiyar da aka kirkira domin Tinubu da APC.

Matashin ya ce ya shiga wannan tafiya da fata da burin ganin an samar wa talakawa adalci, an ba su damar cin moriyar gwamanati.

Har ila yau, ya ce ya so a samu mutunta sadaukarwar matasa da jaruman Kannywood da suka tsaya tsayin daka domin ganin an gyara kasa, amma bayan abin da ya gani da wanda na fuskanta kamar ba don talakawa ake yin tafiyar ba.

Kara karanta wannan

Kurunƙus: Tinubu ya mika fam ga APC, ya zabi wanda zai masa mataimaki a zaben 2027

Dan wasan Kannywood ya fice daga tafiyar Rarara
Matashi dan wasa a Kannywood, Ramadan Booth. Hoto: Ramadan Booth.
Source: Facebook

4. Mansurah Isah

Jarumar Kannywood, Mansurah Isah ta gargadi mawakin jam'iyyar APC, Dauda Kahutu Rarara da matarshi Aisha Humairah.

Hakan na zuwa ne bayan ta sanar da ficewa daga tafiyar Dauda Rarara da ke amfani da ita wajen tallata shugaba Bola Tinubu.

Mansurah Isah ta bayyana cewa ta fito ta yi magana ne a bisa dole ba domin tana so ba, saidai saboda Rarara ya karya alkawari.

Martanin Triple R kan lamarin

Sai dai shugabannin kungiyar sun yi watsi da abin da Rikadawa ya fada, inda suka ce barinsa kungiyar Triple R ya samo asali ne daga muradinsa na kashin kansa.

Sakatare Janar na kungiyar, Ahmad Bifa, ya ce wadanda suka fice daga kungiyar sun fifita bukatunsu na kansu a kan muradun kungiyar.

Ya kara da cewa sun bar kungiyar ne saboda suna son su rika haduwa da 'yan siyasa su kadai domin karbar kudade.

Ya kuma ce babu wanda ya fi Rarara sanin manyan 'yan siyasa a masana'antar Kannywood, cewar Duniyar Kannywood a Facebook.

Kara karanta wannan

Rarara ya karbo Naira miliyan 500, zai shiga Arewa da tawaga tallata Tinubu

Triple R ta yi martani kan matsalar kungiyar
Shugaban kungiyar Triple R, Dauda Kahutu Rarara da mambobin kungiyar. Hoto: @ayshatulhumairah.
Source: Instagram

Mai Sana'a ya musanta jita-jitar mutuwarsa

Mun ba ku labarin cewa jarumin Kannywood, Musa Mai Sana'a, ya yi magana bayan yaɗuwar jita-jitar rashin lafiyarsa da mutuwarsa, inda ya fayyace gaskiyar abin da ya faru.

Jarumin ya bayyana cewa yana cikin ƙoshin lafiya, ya ƙaryata rahotannin da ake yaɗawa tare da yin addu'ar Allah ya shiryar da masu yaɗa ƙaryar.

Mai Sana'a ya kuma bayyana matsayarsa kan tafiyar Triple R Kannywood, yana mai tabbatar da cewa har yanzu yana goyon bayan Shugaba Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.