Rigima Ta Kaure tsakanin Jarumin Kannywood, Lawan Ahmad da Masu Kallon Shirin Izzar So
- Rigima ta ɓarke tsakanin jarumin Kannywood, Lawan Ahmad da masu kallon shirin Izzar So bayan ya sanar da fitowar sabon shirin
- Masu kallo sun soki yadda jarumin ya ci gaba da jan zaren shirin na tsawon shekaru, inda wasu ke cewa sun gaji da kallon shirin
- Sai dai, jarumi Lawan Ahmad ya nuna bacin ransa kan irin maganganun da mabiyan nasa suke yi, inda ya rika martani har da yin zagi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Rigima mai zafi ta kaure tsakanin fitaccen jarumin Kannywood, Lawan Ahmad, da wasu daga cikin masu kallon shirinsa na Izzar So.
Legit Hausa, ta fahimci cewa, da yawa daga cikin masoya Lawan Ahmad sun gaji da shirin Izzar So da yake haskawa tsawon shekara biyar.

Asali: Facebook
Sanarwar Lawan Ahmad ta jawo ce-ce-ku-ce
Masu kallon shirin, sun yi maganganu masu zafi yayin da jarumi Lawan Ahmad ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ya kusa fara haska sabon shirin Izzar So.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, Lawan Ahmad ya ce:
"Izzar So, Takun Farko, kashi na hudu yana nan zuwa a gare ku, bayan dogon lokaci ana hutu."
To sai dai, masu kallon shirin sun yi wa jarumin caa a shashen sharhi, inda da yawansu ke nuna cewa sun gaji da kallon shirin, wasu kuma na kalubalantar jarumin.
Ba sukar shirin ko kalubalantar jarumin ne ya dauki hankalin mutane ba, a'a, yadda aka ga jarumin yana mayar da martani masu zafi ga masoyan nasa, wasu lokutan har da ɗura ashariya.
Cacar bakin Lawan Ahmad Aa masu kallo
Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin sharhin da mutane suka yi a kan sanarwar jarumin, da kuma martanin da shi Lawan Ahmad ya yi:
Real Auwal ya fadawa jarumin cewa:
"Oga da hakura ka yi da fim din nan ka kakama wata sana'a domin kada ai ta lafta ma fim kudi ba masu kallo."
Sai Lawan Ahmad ya ba shi amsa da: "Suna kallo iskanci ne wallahi, suna kallo."
Wani Musa Mk ya yi wa jarumin martani da cewa:
"Gaskiya a cikin mutum 100 zai yi wuya a samu mutum 10 masu kallo, ban ce ba a kallon ba, amma dai gaskiya ba kamar sauran fim din ba, don ni rabon da na kalli Izzar So wallahi tun ana na 83 kuma lokacin ni ne ke daukowa 'yan gidan mu na tura musu, tun da na ji sun bar tambaya ta Izzar So sai wasu fina finan nasan su ma fa sun gaji wallahi."
Wani Hassan Ibrahim Xhaka ya ce:
"Ku rike abun ku, ko biya na za ayi, ba zan sake kallon wannann series din ba, abu ya ki karewa sabo da maita"
Sai Lawan Ahmad ya yi masa martani da cewa:
"Hassan Ibrahim Xhaka dama ba don kai mu ke yi ba"
Abu Dujanah ya ce:
"Tun da Nura ya mutu kuma kuka mutu ai."
Lawan Ahmad ya yi masa martani:
"Abu Dujanah, karya ka ke wallahi, ni na fi samun kudi yanzu ma."

Asali: Facebook
Lawan Ahmad ya fara zagin masu kallo
Zaharadden Kabeeru ne ya yi martani mai zafi, inda ya ce:
"Hauka dai."
Shi ma jarumi Lawan Ahmad, ya yi masa martani mai zafi da cewa:
"Zaharadden Kabeeru, babanka ne ya ke hauka, dan uwarka."
Adam Mustapha ya nuna bai ji dadin kalaman jarumin ba, inda ya ce:
"Ka yi kuskure, a madadin ka bawa mutane hakuri da fahimtar da su ka zo kana zagi, ina sanin addinin ya tafi.?"
Sai Lawan Ahmad ya ba shi amsa da cewa:
"Adam Mustapha, su ma sun yi kuskure, ya za su rinka gaya ma mutane magana? Babu wanda zan ba hakuri."
Kalli sanarwar da martanin mutane a kasa:
Wani ya karbi Musulunci saboda Izzar So
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani Kirista ya karɓi kalmar shahada kuma ya shiga addinin Musulunci, inda ya bayyana cewa kallon shirin Izzar So ne ya ja hankalinsa.
Jarumi Lawan Ahmad, wanda aka fi sani da Umar Hashim a shirin, shine ya bayyana hakan tare da raba bidiyon mutumin yana maimaita kalmar shahada.
Mutumin, wanda aka ce ɗan asalin jihar Cross River ne, ya zaɓi sunan jarumin shirin, Umar, a matsayin sabon sunansa na Musulunci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng