Farin Jakada: Jarumin Kannywood Lawan Ahmad ya fito takarar siyasa a jihar Katsina

Farin Jakada: Jarumin Kannywood Lawan Ahmad ya fito takarar siyasa a jihar Katsina

  • Jarumin Kannywood, Lawan Ahmad, ya tabbatar da shiga tseren takarar mamba mai wakiltar Bakori a majalisar dokokin Katsina
  • Jarumin wanda tauraruwarsa ke haskawa a shirin Izzar So da sunan Umar Hashim, ya fito siyasar ne karkashin jam'iyyar APC
  • Ahmad ya roki mutane su taya shi da addu'a kan lamarin, sannan su yi gum da bakin su matukar ba alheri za su faɗa ba

Katsina - Yayin da siyasar 2023 ke kara kusantowa, masu shirin tsayawa takarar wata kujera na cigaba da fito da kudirinsu fili tare da fara neman goyon bayan al'umma.

Ɗaya daga cikin jarumai a masana'antar shirya fina-finan Hausa Kannywood, Lawan Ahmad, ya sanar da shirinsa na neman takara a zaben 2023 dake tafe.

A wani rubutu da ya saki a shafinsa na Istagram, Lawan Ahmad, ya ce zai nemi takarar ɗan majalisar jiha mai wakiltar mazaɓar Bakori a majalisar dokokin Katsina.

Kara karanta wannan

'Allah ya tabbatar mun' Gwamnan PDP a Arewa ya fadi kujerar da zai fafata a zaben 2023

Jarumi Lawan Ahamd
Farin Jakada: Jarumin Kannywood Lawan Ahmad ya fito takarar siyasa a jihar Katsina Hoto: @lawanahmad
Asali: Instagram

Lawan, wanda tauraruwarsa ke haskawa a Kannywood, kuma furodusan shiri mai dogon zango 'Izzar So' ya buga Fastar takara ya sanya a shafinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jarumin ya ce:

"A gurin Allah muke nema, kuma muna bukatar addu'a, Nagode. Ka faɗi alkhairi ko kuma ka yi gum da bakinka."

Wace jam'iyya ya zabi neman takara?

A fostar da jarumin ya fitar, ya tsaya takarar dan majalisa ne karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulkin Katsina da kuma ƙasa baki ɗaya.

Wannan ba shi ne karo na farko da Jarumin ke fitowa takarar mamba mai wakiltar mazaɓar karamar hukumar Bakori a majalisar dokokin Katsina ba.

A shekarar 2019, Lawan ya nemi tikitin tsayawa takara a APC amma bai samu nasarar tsallake zaben fidda gwani ba.

Da wakilin mu ya tuntubi Jarumi Lawan Ahmad ta wayar salula, ya fara da shaida mana tarihin shigarsa siyasa, inda ya ce:

Kara karanta wannan

Kano: Mummunar gobara ta lamushe kadarorin N18m a Mariri

"Na fara ne da takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Bakori da Ɗanja, amma aka zauna da manya aka ce ya kamata na tafi majalisar jiha, ita ma ba'a samu an nema ba."
"Sai kuma wannan karan, kasan duk wanda ya hito takara ba yin kansa bane, jama'a ne suke kira a fito, shiyasa muka sake fitowa mu sake jarabawa."

Kowane shiri jarumin ke yi na samun nasara, Lawan Ahmd, ya faɗa wa wakilin Legit Hausa cewa ɗan takara baya faɗin manufofinsa sai an fita fagen Kamfen sannan zai fara magana.

A cewarsa ya na neman takarar majalisar dokoki ne ba dan karan kansa ba, yana yi domin al'umma kuma ya bada gudummuwa.

A wani labarin kuma mun tara muku Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa a Najeriya da mukaman da suka nema

Akwai wasu jarumai a masana'antar shirya fina-finan Hausa Kannywood da suka taba neman gwada sa'arsu a fagen siyasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa: Magoya baya sun hada N10m don siyawa zabin Buhari fam

A wannan rubutun mun tattaro muku fitattun jarumai 5 da suka taba neman wata kujerar siyasa a yankunan su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel