Yanzu-Yanzu: Allah ya yiwa daraktan fim din Izzar So, Nura Mustapha Waye rasuwa

Yanzu-Yanzu: Allah ya yiwa daraktan fim din Izzar So, Nura Mustapha Waye rasuwa

  • Fitaccen daraktan fina-finan Kannywood, Nura Mustapha Waye ya riga mu gidan gaskiya, inji rahoton da muke samu
  • An ce daraktan na fim din Izzar So ya rasu yau, kuma za a yi jana'izarsa a unguwarsu a jihar Kano
  • Ya zuwa yanzu dai bamu samu rahoton da ke bayyana ainihin musabbabin rasuwarsa ba, duk da an ce jiya yana nan lafiya

Kano - Yanzu muke samun labarin cewa, ALlah ya yiwa fitaccen daraktan masana'antar Kannywood, Nura Mustapha Waye.

A rahoton da muka samu daga kafar labarai ta DW ya ce, wasu makusanta sun ce an rabu da marigayin da daren jiya cikin koshin lafiya.

Mustapha dai shi ne daraktan wannan shirin mai dogon zango da ya shahara a duniyar Hausawa, wato Izzar So.

Allah ya yiwa Nura Mustapha Waye rasuwa
Yanzu-Yanzu: Allah ya yiwa daraktan fim din Izzar So, Nura Mustapha Waye rasuwa | Hoto: voanews.com
Asali: UGC

Za a yi jana'izarsa ne a makarantar Goren Dutse a jihar Kano.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babban jarumin gaba-gaba a shirin fim din na Izzar So a shafinsa na Instagram ya sanar da rasuwar daraktan a wani rubutu da ya yi.

A cewarsa:

"Innalillahi wainnailaihirrajiun Allah Ya Karbi Rayuwar Nura Mustapha Waye Director IZZAR SO Za Ayi Zanaidarshi Karfe 11 Na Safennan A Gidansa Goren Dutse Primary Insha Allah, Allah Ya Yafe Masa Kurakuransa Amin, Allah Yasa Idan Tamu Tazo Mu Cika Da Imani Amin."

Mawaki Sufin Zamani Zai Saki Bidiyo Da Murya Na Neman Afuwar Matan Kannywood

A wani labarin, jami'an hukumar yan sandan farin kaya, DSS, sun kama mawakin Hausa, Sarfilu Umar Zarewa wanda aka fi sani da Sufin Zamani, rahoton Daily Trust.

Kungiyar masu fina-finai ta MOPPAN ce ta yi korafi kansa saboda wata waka da ya yi mai suna "Matan Fim Ba Su Zaman Aure."

Matan Kannywood ba su ji dadin wakar da Sufin Zamanin ya yi ba inda suka ce cin mutunci ne a gare su. Hakan na cikin sanarwar da sakataren MOPPAN na kasa, Al-Amin Ciroma ya fitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel