Tashin Hankali: Wasu 'Yan Kano Sun Mutu a wajen Tsamo Wayarsu da Ta Fada Masai

Tashin Hankali: Wasu 'Yan Kano Sun Mutu a wajen Tsamo Wayarsu da Ta Fada Masai

  • Mutane biyu, Usman Muhammed da Ibrahim Inuwa, sun mutu a Kano yayin da suka yi ƙoƙarin tsamo wayar salula daga cikin masai
  • Hukumar kashe gobara ta tabbatar da lamarin, tana mai cewa sun shaki iskar guba daga masan wanda ya yi sanadin mutuwarsu
  • Ba wannan ne karo na farko ba; irin hakan ta sha faruwa a Kano, inda mutane da dama suka mutu a kokarin ciro waya daga masa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - A ranar Asabar, 21 ga Yuni, 2025, wani mummunan lamari ya faru a kauyen Bazabe da ke ƙaramar hukumar Albasu ta jihar Kano.

An ce wani Usman Muhammed da abokinsa Ibrahim Inuwa, dukkansu ’yan shekara 40, sun rasu yayin da suke ƙoƙarin tsamo wayar salula daga cikin masai.

Mutane 2 sun mutu a kokarin a kokarin da suka yi na ciro wayar salula daga cikin masai
Taswirar kasar Najeriya da ke nuna jihar Kano. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Maza 2 sun makale a masai garin ciro waya

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, 22 ga Yuni, 2025, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce ofishin kashe gobara na Takai ya karɓi kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:16 na safe daga wani jami’in ‘yan sanda mai suna Sufeta Auwalu.

Sufeta Auwalu ya shaidawa hukumar cewa wasu maza biyu sun makale a cikin masai, inda nan take aka tura tawagar ceto zuwa wurin.

An rahoto cewa Usman Muhammed ne ya fara shiga cikin masan don ciro wayar sa da aka fi sani da "Indon Kauye" da ta faɗa ramin.

Usman da Ibrahim sun mutu bayan shiga masai

Jaridar Punch ta rahoto cewa bayan Usman ya kasa fita, sai Ibrahim Inuwa ya ɗaura igiya a jikinsa ya shiga don ceto shi, amma shima ya makale a ciki tare da suma.

Tawagar ceto ta fito da su dukkansu a sume, inda aka garzaya da su asibiti, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsu sakamakon shakar guba daga masan.

An mika gawarwakin ga shugaban ‘yan sanda na Albasu, SP Kabiru Magawata, domin gudanar da bincike da daukar sauran matakai da suka dace.

Wannan lamari ya sake jaddada haɗarin da ke tattare da shiga ramin masai ba tare da kariya ko horo na musamman ba.

An ce irin waɗannan wurare na ɗauke da iskar guba kamar methane da hydrogen sulfide, wanda ke jawo sumewa da mutuwa cikin kankanin lokaci.

Hukumar kashe gobara ta ce ta tsamo mutanen biyu da suka fada masai amma an tabbatar da mutuwarsu a asibiti
Jami'in hukumar kashe gobara ta jihar Kano reshen Sharada. Hoto: @KanoChronicle
Asali: Facebook

Mutum 3 sun mutu a masai a Kano

Ba wannan ne karo na farko da irin wannan lamarin ya faru a jihar Kano ba, domin ko a watan Afrilun 2024, wasu mutum uku sun mutu sanadiyyar shiga masai.

A lokacin an rahoto cewa Malam Danjuma, da ɗansa Ibrahim, da makwabcinsu Aminu Gaye, sun mutu a cikin masai a kauyen Yar’Gwanda da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa yayin da suke ƙoƙarin tsamo waya.

Wani mutum na huɗu ne kawai aka ceto da rai a wannan lokacin, kamar yadda rahoton Vangaurd ya nuna.

Bakano ya mutu a garin tsamo waya a masai

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani mutum mai suna Muazu Garba mai shekaru 40, ya mutu cikin masai a kokarin tsamo wayarsa a ƙaramar hukumar Nassarawa.

An gano yadda Mu'azu Garba, ya shiga ramin masai don ciro wayarsa, amma ya kasa fitowa, daga bisani aka ceto shi ranga-ranga, sannan rai ya yi halinsa.

Ko lokacin da 'yan kwana-kwana suka isa wurin sun tarar da gawar mutumin daga baya suka mika gawarsa ga shugaban gundumar Jigirya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.