Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa a Najeriya da mukaman da suka nema

Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa a Najeriya da mukaman da suka nema

  • Akwai wasu jarumai a masana'antar shirya fina-finan Hausa Kannywood da suka taba neman gwada sa'arsu a fagen siyasar Najeriya
  • A wannan rubutun mun tattaro muku fitattun jarumai 5 da suka taba neman wata kujerar siyasa a yankunan su
  • Daga cikinsu har da furodusan fim ɗinnan mai farin jini 'Izzar So' wato Lawan Ahmad daga jihar Katsina

Ƙano - A cikin masana'antar fina-finan Hausa wacce aka fi sani da Kannywood, akwai wasu jarumai da suka taba kokarin nuna bajintarsu a fagen siyasa.

Waɗannan jarumai sun fito takara a matakai daban-daban na yankunansu, kuma a dokar ƙasa kowa na da damar fitowa takara matukar ya cike ƙa'idojin hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC.

Jaruman Kannywood
Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa a Najeriya da mukaman da suka nema Hoto: aminiya.dailytrust.com
Source: UGC

Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasu jarumai 5 daga cikin Kannywood waɗanda suka taba fitowa takarar siyasa a Najeriya.

Read also

Da Dumi-Dumi: Mambobin Jam'iyyun Hamayya Sama da 5,000 Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC

Ga sunayen jaruman da kuma mukaman siyasa da suka nema, kamar yadda Aminiya ta rahoto.

1. Hamisu Iyantama

Hamisu jarumi ne da aka jima ana fafatawa da shi a masana'antar Kannywood, kuma ya taba fitowa takarar gwamnan jihar Kano a shekarar 2007.

Jarumin ya fito takarar ne ƙarƙashin jam'iyyar ND, amma Malam Ibrahim Shekarau na ANPP ne ya ƙashe zaɓen a wannan lokaci.

2. Alasan Kwalle

Alasan sananne ne a Kannywood musamman a shirye-shiryen barkwanci kuma yana ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki a masana'antar.

Alasan Kwalle
Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa a Najeriya da mukaman da suka nema Hoto: aminiya.dailytrust.com
Source: UGC

Jarumin ya nemi takara da dama, cikinsu harda takarar shugaban ƙaramar hukumar Ungogo da ya nema a shekarar 2007 ƙarkashin PDP. A wannan lokaci ya kare a matsayin ɗan takarar mataimaki.

Hakanan kuma ya tsaya takarar kansila a gundumarsa Bachirawa dake Ungogo karkashin inuwar jam'iyyar APC a shekarar 2015.

Read also

Matar shugaban ƙasa Aisha Buhari ta yi magana mai muhimmanci kan Matan Gwamnoni

3. Nura Hussain

Nura na ɗaya daga cikin jaruman Kannywood da suka jima ana damawa da su, ya fito takarar Kansila a mazaɓar Yakasai, ƙaramar hukumar Birni da Kewaye, cikin jihar Kano, a shekarar 2007.

4. Abba El-Mustapha

El-Musatapha ko Abba Ruda kamar yadda aka fi saninsa, jarumi ne da ya yi tashe kuma ya jima a masana'antar shirya fina-finan Hausa.

Abba El-Mustapha
Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa a Najeriya da mukaman da suka nema Hoto: aminiya.dailytrust.com
Source: UGC

Abba ya taba neman tikitin takarar ɗan majalisar jiha mai wakiltar mazaɓar Gwale ta jihar Kano, karkashin jam'iyyar PDP a 2015.

Sai dai Abba Ruda bai samu nasara ba, domin bai samu tikitin tsayawa takarar ba tun a wurin zaɓen fidda gwani.

5. Lawan Ahmad

Wannan jarumi ya jima tauraruwarsa na hasakawa a Kannywood, a halin yanzun shine furodusan fim mai dogon zango 'Izzar So.'

Lawan Ahmad
Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa a Najeriya da mukaman da suka nema Hoto: @lawanahmad
Source: Instagram

Lawan Ahmad ya taba neman tikitin takarar ɗan majalisar jihar Katsina mai wakiltar mazaɓar Bakori ƙarakashin jam'iyyar APC amma bai samu tikitin ba.

A wani labarin kuma mun tattaro muku Sabbin zafafan Hotunan Jaruma Rahama Sadau a wurin daukar fim a Bollywood Indiya

Read also

Sabbin zafafan Hotunan Jaruma Rahama Sadau a wurin daukar fim na Bollywood Indiya

Tun a baya dai Sadau ta buga hotuna a dandalinta na sada zumunta, inda tace tana aikin shirin fim da masana'antar Bollywood.

Rahama Sadau, ta saba jawo cece kuce kan shigar da bata dace da addininta ba kuma ta dora a kafar sada zumunta.

Source: Legit.ng

Online view pixel